02
Apr
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Shari'a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya ya yi watsi da ƙarar kare haƙƙin ɗan-adam da Omoyele Sowere ya shigar akan Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, darakta janar ɗinta da kuma dandalin Meta da aka fi sani da Facebook. Da yake gabatar da hukunci, Alƙali Umar ya ce babu ɗaya daga cikin buƙatu uku da Sowore ya gabatar da suka cancanci a biya don haka ya yi watsi da ita a sakamakon rashin nagarta. Sowore ya yi ikirarin cewa dandalin Facebook ya yi aiki da umarnin DSS wajen sauke rubutun da ya…
