Babaji

5689 Posts

Tashin jirgi da dare bai dace da yanayi mai kyau ba – Fadar Shugaban Ƙasa kan ganawar Tinubu da ‘yan Filato a ‘yan mintuna

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilan da suka sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gana da waɗanda hare-haren jihar Filato ya shafa a filin jirgin sama maimakon shiga cikin garin Jos. A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce jadawalin shugaban ƙasa na ranar Alhamis ya haɗa da manyan ayyuka biyu; karɓar baƙuncin shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, da kuma tafiya zuwa Iperu a Jihar Ogun. Sanarwar ta ce bayan samun bayani daga gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, shugaban ƙasa ya dakatar da shirinsa…
Read More

Sa hannuna aka kwaikwaya, inji shugaban tsagi na ADC Nafi’u Bala yayin ƙaryata takardar murabus

Shugaban tsagi na jam’iyyar ADC na ƙasa, Nafi'u Bala ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi murabus daga muƙaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa. Bala ya bayyana cewa, takardar murabus ɗin da ake yaɗawa ba tasa ba ce, yana mai zargin cewa an ƙirƙiri sa hannunsa domin yaɗa rikici a cikin jam’iyyar. Ya jaddada cewa har yanzu yana kan kujerarsa, kuma bai ajiye aiki ba ko kaɗan. Wannan martani nasa na zuwa ne bayan hukuncin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta yanke a ranar Laraba, dangane da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar ADC.…
Read More

FIFA na neman faɗaɗa adadin ƙasashen gasar Kofin Duniya zuwa 64

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ta tabbatar da cewa ta fara aikin faɗaɗa adadin ƙasashen da za su fafata a gasar Kofin Duniya na 2030 zuwa 64 domin ƙara wa gasar armashi. A cewar The York Times, Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na ƙasar Uruguay, Ignacio Alonso ne ya gabatar da shawarar a karom fari a Maris ɗin shekarar 2025. Shugaban FIFA Gianni Infantino ya bayyana shawarar da matsayin abin da ke buƙatar a yi wa karatun ta nitsu da sharhi mai faɗi. Matuƙar aka amince da wannan shawara, ƙasashen da…
Read More

ADC ta bijire wa INEC, ta sanar da ranar babban taro da wasu ayyuka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar adawa ta ADC ta tirje akan cigaba da shirinta na gudanar da babban taro da wasu taruka duk da cewa Hukumar Zaɓe (INEC) ta ƙi amince wa shugabancinta. A wata sanarwa da Sakataren Shirye-shiryenta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fita a yau Juma'a, ADC ta ce za gudanar da tarukan nata daga ranar 7 zuwa 14 ga watan nan na Afrilu, 2026. Ya ce, za a fara ne da tantance 'yan takara sannan a kammala da babban taro na ƙasa. Don haka ne ta sanar da ɗaukacin mambobinta duk da gargaɗin INEC akan…
Read More

Shugaban sojoji ya jagoranci sauran jagororin tsaro zuwa Filato don dawo da zaman lafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, Waidi Shaibu ya jagoranci tawagar jagororin tsaro zuwa Jos, Babban Birnin Jihar Filato domin duba matakin halin tsaro biyo bayan rikicin da ya ɓarke a kwanan nan da ke nema haddasa fitina ga zaman lafiyar al'umma. Ziyarar na zuwan ne a daidai lokacin da al'amarin tsaro ke neman taɓarɓarewa a sassan jihar yayin da jami'an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan al'amarin domin kauce wa yaɗuwar rikici a faɗin jihar. A saboda haka ne Laftanal Janar Waidi Shaibu, ya amince da tura ƙarin dakarun soji sama da guda…
Read More

EFCC na ƙoƙarin tabbatar da ƙwace kadarori 57 da aka danganta da Malami

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta nemi wata babbar kotu da ta bayar da umarnin ƙwace wasu kadarori guda 57 da ake danganta su da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, har abada. EFCC ta ce, an shigar da wannan buƙata ne ƙarƙashin Sashe na 17 na dokar Advance Fee Fraud and Other Fraud-Related Offences Act, 2006, inda hukumar ta bayyana kadarorin a matsayin waɗanda ake da ƙwarin gwiwar zargin cewa sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka. Hukumar ta jaddada cewa binciken da ta gudanar ya nuna alamun cewa kadarorin…
Read More

Kano: Rikicin APC ya yi ƙamari yayin da sakataren walwala ya bi sawun Gawuna wajen fita a jam’iyyar

A ranar Alhamis Sakataren walwala na jam’iyyar APC a Jihar Kano, Bashir Tijjani Maisango, ya yi murabus daga jam’iyyar inda ake sa ran zai koma jam’iyyar ADC. Maisango, wanda a baya ya riƙe mukamin mataimakin sakatare a jam’iyyar, na daga cikin manyan jagorori masu tasiri da kuma masu jan hankalin jama’a a matakin kasa a Kano. A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai taken “Murabus na radin kai daga jam’iyyar APC” wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar na jiha, ya bayyana godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta. Ya ce: “Ni, Bashir Tijjani Maisango, ina…
Read More

Kira ga tsige Farfesa Amupitan cin fuska ne ga dimukraɗiyya – INEC ga ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi tir da kiraye-kirayen tsige Shugabanta Farfesa Joash O. Amupitan, tana mai tirjewa akan hakan ya saɓa wa dokar ƙasa kuma barazana ce ga 'yan zaman kan tsarin zaɓen Nijeriya. A wata sanarwa da ta fitar a daren Juma'a a Abuja, hukumar ta ce sukar da wasu 'yan siyasa ke mata da zargin ta akan zama 'yar wata jam'iyya ba daidai ba ne, tana mai cewa dukkan ayyukanta suna bisa doka da tsarin shari'a. INEC ta bayyana cewa batutuwan da suka shafi naɗi, wa'adi da tsige shugaba da…
Read More

Kashe-kashen Filato: Hakan ba zai sake faruwa ba, inji Tinubu ga iyalan waɗanda iftila’in ya afka wa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ci alwashin cewa ba za a sake ganin tashin hankalin da aka gani a garin Jos da ke Jihar Filato ba. Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci jihar domin yi wa jama’ar jihar jaje musamman ga iyalan waɗanda iftila'in ya shafa. Shugaban wanda ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar a tashar jiragen saman Heipang, ya ce za su yi iya bakin ƙoƙarin su domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar. Shugaban Tinubu da ya ziyarci jihar da misalin karfe 5 na yammacin yau, a kan hanyar ta zuwa…
Read More

Tinubu ya umarci a sanya kyamarorin tsaro 5,000 a sassan Filato

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin girka sama da kyamarori 5,000 a Jihar Filato domin inganta tsaro bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a Jos. Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da shugabannin siyasa da na gargajiya a Jos, bayan harin Palm Sunday da ya kashe fiye da mutane 27 a Angwan Rukuba. Ya kuma umarci hafsoshin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata harin, tare da jaddada cewa dole ne a gano masu laifin. Kazalika, Tinubu ya sanar da shirin kafa kwamitin da zai tantance asarar da wadanda abin ya shafa suka yi…
Read More