Babaji

5689 Posts

Mutum ɗaya ya rasu, yayin da aka ƙona mai shago akan gari da ruwan leda a Katsina

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Katsina ta kama mutane huɗu da hannu a aikin dabanci da ya yi ajalin mutuwar wani KC Joe a ƙauyen Kokami da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja. A wata sanarwa da ya fitar, Kakakin rundunar, Abubakar Sadiq ya ce a yanzu haka mutane huɗu suan hannun hukumar kuma ana gudanar da bincike akansu. Ya bayyana cewa, al'amarin ya faru ne bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin marigayin da wani mai suna Ibrahim Auwal wanda Joe ya halaka, lamarin da ya fusata matasa har suka yi sanadiyyar mutuwar Joe. Faruwar haka…
Read More

Atiku ya yi hayar kamfanin Amurka kan biliyan N1.65 don ɗaga darajarsa akan Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ba wani kamfanin ƙwararru na Amurka mai suna Von Batten-Montague-York kwangila, domin karewa da inganta martabarsa a Amurka. Rahotanni sun nuna cewa kwangilar da aka ƙulla tsakanin ɓangarorin biyu na da darajar dala miliyan 1.2, inda ake sa ran kamfanin zai taimaka wajen ƙarfafa sunan Atiku tare da tinkarar tasirinsa daga Gwamnatin Tarayya. An ƙulla wannan yarjejeniyar ne a ranakun 9 da 10 ga Maris, 2026, tsakanin manajan kamfanin, Karl Von Batten, da kuma wani ɗan siyasar Nijeriya mai suna Fabiyi Oladimeji, kamar yadda TheCabel ta ruwaito.…
Read More

Matar tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hajiya Hadiza Attahiru Jega, wadda matar tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa INEC, Farfesa Attahiru Jega ne ta rasu a yau Lahadi, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Marigayiyar ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya, lamarin da ya janyo alhini da jimami a tsakanin iyalai, abokai da al’ummar ƙasa baki ɗaya. Hajiya Hadiza Jega ta kasance mace mai kamun kai da kishin al’umma, wacce ta taka rawar gani wajen tallafa wa harkokin ilimi da zamantakewa musamman a lokacin da mijinta ke riƙe da mukaman gwamnati da na jami’a. Farfesa Attahiru Jega, wanda ya…
Read More

Tinubu ya ƙaddamar da filin jiragen sama a Ogun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da filin jiragen sama, wato 'Gateway Cargo International Airport', wanda Gwamnatin Gwamnan Ogun Dapo Abiodun ta gina a jihar. Haka kuma Shugaban ya ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu mallakar kamfanin Gateway Airline. Ya ce: “Jarinmu domin al’ummarmu ne. Ababen more rayuwar da muke ginawa suna nuna imaninmu ga ƙasarmu, da kuma cewa tubalin yau na nufin arziƙin gobe. Na gode muku duka bisa fahimtarku." An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne cikin gagarumin yanayi a Ƙaramar Hukumar Iperu, inda manyan jami’an gwamnati da shugabanni suka halarta. Daga cikin…
Read More

Mu na aiki tuƙuru wajen kawo ƙarshen ta’addanci da garkuwa a Nijeriya – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa tana nan daram kan baƙarta na ganin bayan ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane da suka addabi sassan ƙasar nan, yana mai cewa ba za su taba nuna rago ko karaya ba. Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ƙalubalen tsaro, inda ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ana nan ana ƙara azama wajen samar da dabarun yaƙi na zamani domin kakkabe ɓatagari. Bayanai sun nuna cewa Shugaba Tinubu ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa shi ne babban nauyin da ya rataya a wuyansa, saboda haka ba…
Read More

Tinubu ya ƙaddamar da sabon babban ofishin Kwastom a Ogun

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabon ginin ofishin Hukumar Kwastom mai darajar Naira biliyan 73 a Jihar Ogun a wani mataki da ake ganin zai ƙarfafa ayyukan hukumar da kuma inganta ƙwarewar ma’aikatanta. A yayin taron ƙaddamarwar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sabon ginin zai taimaka wajen ƙara inganci a harkokin kwastam musamman wajen sanya ido akan shigo da kaya da kuma hana safarar haramtattun kayayyaki. Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa hukumomin gwamnati domin su yi aiki yadda ya dace da zamani. Sabon ofishin zai samar da ingantattun kayan aiki na zamani da kuma muhalli mai…
Read More

INEC ta gargaɗi ADC akan gudanar da babban taro

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyar adawa ta ADC kan dagewar da take yi na gudanar da taronta na kasa da babban taro duk da umarnin kotu da ya hana ta daukar irin wannan mataki. INEC ta bayyana cewa 2cigaba da gudanar da tarukan duk da umarnin kotu na iya janyo mummunan hukunci na doka, har ma da yiwuwar haramta wa jam’iyyar shiga zaɓuka masu zuwa. Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Juma’a, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya nesanta hukumar daga rikicin cikin gida da ke addabar ADC…
Read More

Zan ba su horo, na gyara bindigoginsu, inji ɗan sanda mai ritaya da ya yi barazanar shiga Boko Haram kan rashin biyan sa fansho

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani tsohon jami'in rundunar 'yan sanda ya janyo hankalin jama'a tare da nuna fargaba bayan ya yi barazanar shiga ƙungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram saboda ƙorafe-ƙorafen da suka shafi kuɗaɗensa na fansho. Da yake jawabi a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, Tsoho jami'in ya yi gargaɗin ɗaukar mummunan mataki matuƙar ba a warware masa matsalar fanshonsa ba. "Idan ba a yi komai ba game da wannan, zan koma ɗaya ɓangaren kuma na shiga Boko Haram, in riƙa taya su gyara bindigoginsu da ba su horo", inji shi. Ya bayyana…
Read More

Ministar Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Juma'a Ministar Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, ta yi murabus daga muƙaminta na minista. Hakan na zuwa ne bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar ga masu niyyar tsayawa takara a 2027 da ke riƙe da muƙaman gwamnati na su ajiye domin su mayar da hankali akan abu ɗaya. Ta sanar da murabus ɗin nata ne a wani rubutu da ta wallafa ta shafukan sada zumunta, inda ta gode wa shugaban ƙasa da ɗaukacin ’yan Nijeriya bisa damar da aka ba ta. Onyejeocha, ta ce ta ɗauki aikin a matsayin babban gata, tare…
Read More

Koma wa dimukraɗiyya tamkar dawo da mulkin mallaka ne – Shugaba Traore ga ‘yan Burkina Faso

Shugaban gwamnatin mulkin soja ta ƙasar Burkina Faso, Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa tsarin dimokuraɗiyya irin na ƙasashen Yamma bai dace da ƙasarsa ba, yana mai danganta shi da wani nau’in bautar zamani. Traoré ya yi wannan furuci ne a wata hira da ya bayar a daren Alhamis, yayin da ake cika shekara guda da ƙaddamar da wata manufa mai taken Juyin Juya Halin Ci gaban Jama’a (RPP), wadda ya ƙirƙira a watan Afrilun bara. A cewarsa, manufar RPP an gina ta ne domin tabbatar da cikakken ‘yancin kai na ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arziki mai dogaro da kai,…
Read More