Babaji

5689 Posts

Mutane huɗu sun rasu yayin da ‘yan bindiga suka farmaki ƙauyukan Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane huɗu ne suka rasu a wani hari da aka kai a wasu ƙauyuka sa ke Gundumar Gebbe a Ƙaramar Hukumar Shanga ta Jihar Kebbi. Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun fito ne daga maɓoyarsu da ke dajin Wawa a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, wadda ke da iyaka da ƙauyukan da lamarin ya shafa a Shanga. Haka kuma, a yayin harin ne aka ƙone wasu gine-gine da ke ƙauyukan Kalkami, Tungar Bori da Kawara da sauransu. Bayanai sun tabbatar da cewa ƙari akan Kalkami, maharan sun kuma ƙone ƙauyen Kawara a…
Read More

Bom ya yi ajalin direba da matuƙin babur a Neja yayin farmakin ‘yan bindiga

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane biyu ne suka rasu yayin da ake zargin 'yan ta'adda ne suka dasa bom akan hanyar Lumma-Babanna da ke Ƙaramar Hukumar Borgun Jihar Neja. Al'amarin ya faru ne da misleading ƙarfe 2 na rana a ranar Lahadi, wanda ya yi ajalin wani direba da wani matuƙin babur da ya rasu bayan fashewar bom ɗin. A cewar hukumomi, direban yana ƙoƙarin neman wata hanya ce domin ficewa daga yankin a lokacin da al'amarin ya faru sakamakon hawa kan abin fashewar da motarsa ta yi, wanda ya haddasa mummunan iftila'i. An gano cewa, ta…
Read More

An halaka mutum uku yayin da jami’an tsaro suka daƙile hari a Jos, an kama wanda ake zargi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin wani hari da wasu 'yan bindiga suak yi yunƙurin kai wa a yankin Hyeipang da ke Jos a Jihar Filato, yayin da jami'an tsaro suka yi nasarar daƙile harin da kuma cafke mutum ɗaya da ake zargi da hannu aciki. Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a daren Lahadi a ƙauyen Pwomol da ke gundumar Heipang, inda aka kai farmaki kan matasa yan sa-kai da ke tsaron al’umma. Wani mutum ɗaya ya jikkata kuma yana karɓar magani a asibiti. Haka kuma, a safiyar Litinin,…
Read More

An kama mutane biyar yayin da sojoji ke binciken harbin kuren da ya yi ajalin ‘yar shekara 14 a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an tsaro da aiki a ƙarƙashin rundunar atisayen HADIN KAI sun yi nasarar kama mutane biyar da ake zargi da hannu a harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya yi ajalin wata budurwa a yankin Ngomari da ke Jihar Barno a Arewa maso Gabashin Nijeriya. Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, lokacin da wasu jami’an tsaro na sa-kai, waɗanda ke yin rakiya ga wani shugaban ƙaramar hukuma, su ka yi harbi sama yayin wani bikin aure a rukunin gidajen malamai na Umaru Musa Yar’Adua. Rahotanni sun bayyana cewa…
Read More

Kamaru: Shugaba Paul biya mai shekaru 93 ya naɗa ɗansa a mataimakin shugaba kuma shugaban sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya ya naɗa ɗansa Frank Emmanuel Biya a matsayin Mataimakin Shugaba kuma Shugaban Rundunar Sojin ƙasar, matakin da ya mayar da tsarin siyasa da jagorancin sojin ƙasar na bai-ɗaya. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici da taƙaddamar zaɓe ke ƙara ta'azzara rikicin siyasa a faɗin ƙasar. Nadin, wanda aka sanar a cikin wata doka a hukumance mai kwanan wata 4 ga Afrilu 2026, ya kuma ayyana Franck Biya a matsayin Wakili na Minista a Ma'aikatar Tsaro, wanda hakan ya sanya shi a tsakiyar tsarin tsaron Kamaru. Matakin…
Read More

ADC ta musanta jita-jitar murabus, ta ce David Mark na ƙoƙarin kai ta ga nasara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar adawa ta ADC ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Shugabanta na Ƙasa na tsagi, Sanata David Mark ya sauka daga mukaminsa, tana mai bayyana su a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama'a. A wata sanarwa da Ofishin Yaɗa Labarai na Shugaban Jam’iyyar ya fitar, ADC ta bayyana jita-jitar a matsayin ƙage mai muni da masu yaɗa farfaganda marasa hankali, raunana, kuma marasa tunani suka ƙago. Sanarwar ta tabbatar da cewa Sanata David Mark na nan daram a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar na Kasa, tare da jaddada cewa babu wani…
Read More

INEC ta dakatar da shirin tantance masu zaɓe

Hukumar Zaɓe Ƙasa INEC, ta umarci Kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) da su dakatar da duk wani shiri da tallace-tallace da suka shafi shirin sake tantance masu kada kuri’a a fadin kasar nan. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da tattaunawa kan yadda za a inganta tsarin rajistar masu kada kuri’a da kuma tabbatar da sahihancin bayanan masu zabe kafin babban zaben kasa mai zuwa. A cewar majiyoyi daga cikin hukumar, an umurci dukkan ofisoshin INEC na jihohi da su dakatar da duk wani shiri da aka fara domin gudanar da wannan aikin, har sai…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya amince da ware tiriliyan N3.3 don biyan bashin lantarki a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani tsari na biyan tsohon bashin Naira tiriliyan 3.3 da nufin gyara matsalar wutar lantarki a Nijeriya da akajima ana fama da ita. A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, an ce bashin ya samo asali ne tun daga watan Fabrairun 2015 zuwa Maris 2025, kuma an amince da wannan adadi ne bayan tantancewa domin tabbatar da adalci wajen biyan sa. Tuni aka fara aiwatar da biyan bashin, wanda kimanin kamfanonin DisCos guda 15 ne aka yi yarjejeniyar da su akan Naira tiriliyan 2.3.…
Read More

Jami’ai huɗu da mafarauci sun rasu yayin da Boko Haram ta farmaki ofisoshin ‘yan sanda a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne a Jihar Borno, sun farmaki ofisoshin 'yan sanda guda biyu a Nganzai da ke Ƙaramar Hukumar Nganzai da Damsak a Ƙaramar Hukumar Mobbar. A yayin harin, wanda ya auku a jiya Asabar, an ce mayaƙan sun harba ababen fashewa na gurnet da wasu muggan makamai, sannan sun yi damejin wani sashe na ofishin tare da ƙone wata motar yaƙin jami'ai da ta jima a ajiye. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Nahum Kenneth Daso ya bayyana haka a wata takarda a ranar Asabar, inda ya ce 'yan…
Read More

Kaduna: Harin ‘yan bindiga ya yi ajalin mutane bakwai da sace wasu a Kachia

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a ƙauyen Ariko da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna sun farmaki mutane a coci guda biyu yayin da ake bikin Easter a yau Lahadi, inda suak halaka mutane bakwai da yin garkuwa da wasu da dama. Al'amarin ya faru ne a safiyar yau Lahadi, wanda ya jefa jama'ar yankin cikin firgici da jimami. Kansilan yankin Awon da ke Gundumar Ariko, Mark Bawa ya tabbatar da harin ga manema labarai ta wayar tarho. A cewarsa, cocin First Ekwa da St. Augustine Catholic ne aka kai wa…
Read More