Babaji

5689 Posts

Sanata Kabiru Gaya ya fice daga APC

Screenshot Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yanayi na ci-gaban siyasa a Jihar Kano, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon sanata, Kabiru Gaya ya fice daga jam'iyyar APC a hukumance. Gaya, wanda ya riƙe muƙamin sanatan Kano ta Kudu, ya sanar da matakin nasa na barin jam'iyyar ne a wata wasiƙa zuwa ga shugaban yankinsa na Gaya ta Arewa a Ƙaramar Hukumar Gaya ta Jihar Kano. Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa shawarwari daga 'yan mazaɓarsa da kuma ganin dacewar hakan daga gare shi na ya bar jam'iyyar. Ya kuma bayyana godiyarsa ga jam'iyyar bisa…
Read More

Sojoji da Jami’ar Jos sun ƙaryata jita-jitar rikici a farfajiyar jami’ar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'ar Jos da Rundunar Sojin Nijeriya sun yi watsi da rahoton ƙarya da ake yaɗawa a kafafen Soshiyal Mediya da ke zargin cewa ana rikici a farfajiyar jami'ar, inda suka bayyana hakan a matsayin yunƙurin yaɗa abin da zai firgita al'umma. Rahoton, wanda aka baza da ke ɗauke da yanayin ɓarkewar rikici a jami'ar, ya yi ikirarin cewa ƙuncin da ɗalibai suke ciki ya rikiɗa ya zama tashin-tashina. Wani bincike daga THE STAR da tabbatarwa daga hukumomin jami'ar sun nuna cewa babu wani rikici da ke faruwa a jami'ar, inda hasali ma ana cigaba…
Read More

Rundunar sojoji ta yi wa tsohon soja martani kan ikirarin mallakar kaki da rigar kariya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce zargin da wani tsohon soja da aka kora mai suna Rotimi Olamilekan ya yi na cewa sojoji na sayen kayan aiki da kansu ciki har da rigunan aiki, hulunan kariya da rigunan kariya ba gaskiya ba ne. Da take martani akan zargi wanda aka yaɗa a kafafen sada zumunta da na labarai, rundunar ta ce tana ba da muhimmanci sosai ga jin daɗi, tsaro da kariyar jami’anta a kodayaushe. A wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama’ar rundunar ta riƙo, Kanal Appolonia Anele, ta fitar a ranar Talata, rundunar…
Read More

Matatar Ɗangote ta ƙara farashin fetur da dizal

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matatar Mai ta Ɗangote ta ɗaga farashin fetur da Naira 75, inda kowace lita ta kai N1,275, yayin da na dizal kuma ya ƙaru da Naira 200, wato ya kai N1,950. Wani jami’i a matatar ya shaida wa manema labarai a daren Talata cewa wannan ƙara farashi ya samo asali ne daga canjin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da yanayin kasuwa a cikin gida. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da masu amfani ke fuskantar tashin farashin kayan masarufi, inda wannan ƙara zai iya ƙara wa farashin sufuri da sauran kayayyaki nauyi.…
Read More

Filato: Ɗan aji uku a jami’a ya rasu yayin harin dare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu 'yan bindiga sun yi wa wani ɗalibin Jami'ar Ilimi ta Tarayya da ke Pankshin kwanton-ɓauna tare da halaka shi a ƙauyen Dum da ke Gundumar Bachi a Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato. Rahotanni sun bayyana cewa, ɗalibin, mai suna Badung Sunday Alamba ɗan shekara 29 ya rasu ne a lokacin da maharan suka yi kwanton ɓauna a mashigar ƙauyen, inda suka buɗe wa wasu 'yan ƙauyen biyu wuta. Ɗaya daga cikinsu ya samu tsira yayin da shi kuma Alamba ya rasa ransa. An ce shi kaɗai mahaifiyarsa ta haifa, wanda hakan ya…
Read More

Ƙungiyar Likitoci ta dakatar da yajin aiki, ta yi gargaɗin ɗaukar sabon mataki a 21 ga Afrilu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Ƙasa (NARD), ta dakatar da yajin aikin gama-gari da ta tsunduma a yau Talata. Da yake ganawa da manema labarai a ranar, Shugaban NARD, Mohammed Usman Suleiman an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da majalisar zartarwar ƙungiyar, inda a nan aka umarci dukkan likitoci su koma aiki da misalin ƙarfe 8 na safiyar ranar Laraba. Suleiman ya bayyana cewa, NARD ta samu tabbaci daga Gwamnatin Tarayya akan sauya matakin janye aiwatar da tsarin biyan alawus ga mambobin na PAT, wanda zai fara a watan Afrilun 2026. Akan…
Read More

Yusuf Buhari ya ayyana aniyar tsaya wa takarar kujerar Majalisar Wakilai

Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wato Yusuf Buhari (Talban Daura), ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai a zaɓen 2027. Hakan na kunshe ne cikin wata wasiƙa da ya sanya wa hannu da kansa mai ɗauke kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, mai taken bayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar mazaɓar Sandamu/Daura/Mai’adua a ƙarƙashin jam’iyyar APC. A cikin wasiƙar, ya ce bayan tuntuba da dama, ya yanke shawarar tsayawa takara domin bayar da gudummawar sa wajen samar da ingantaccen shugabanci, tare da kawo ci gaban ababen more rayuwa da tallafin jama’a a yankin. Bayyanar sa ta zo…
Read More

Likitoci sun fara yajin aiki a yau kan bashin da suke bi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yajin aikin da Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Ƙasa (NARD) ta sanar da farawa ka iya jefa fannin lafiya a Nijeriya cikin mawuyacin hali a matakin asibitocin jihohi da na ƙasa. NARD ta ɗauki wannan mataki ne na sai baba-ta-gani a fadin ƙasar sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na dakatar da aiwatar da gyaran fuska na alawus-alawus na ƙwararrunta. Babban sakataren kungiyar, Shuaibu Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan da kungiyar ta gudanar da wani taron majalisar zartarwar ta a ranar Asabar. Ya bayyana cewa, yajin aikin zai fara ne da…
Read More

Yanzu-yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi, Usman Ankwai ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kakakin Majalisar Dokoki a Jihar Kebbi, Hon. Muhammad Usman Ankwai ya rasu. Tuni dai 'yan uwa da abokan arziƙi daga takwarori da 'yan siyasa suka riƙa miƙa ta'aziyyarsu ga iyalan mamacin a jihar. Ankwai shi ne kakaki a majalisar dokokin jihar ta 10, kuma yana wakiltar mazaɓar Zuru. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a san a wani hali yake ba gabanin rasuwar ba.
Read More

Bayan jan layi da Kwankwaso, Gwamnan Kano na neman haɗa kai da Shekarau don faɗaɗa dabarun siyasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya fara tattaunawa akan shawarwarin siyasa da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau a wani yanayi na ƙarfafa matsayinsa yayin tunkarar zaɓen 2027. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sauye-sauyen tafiyar siyasa a Kano, wadda ɗaya ce daga cikin jihohin Nijeriya da harkar siyasa ke da gagarumin tasiri acikin al'umma. Fasalin siyasa a jihar ya sauya ne bayan da Gwamna Abba ya jingine tafiyar uban tafiyar siyasarsa kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da ficewa a jam'iyyar NNPP da koma wa mai…
Read More