08
Apr
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masu ruwa da tsaki na jam’iyyun PDP da ADC sun shiga wani taron gaggawa domin tattaunawa kan matsalolin da jam’iyyun adawa ke fuskanta. Taron, wanda ke gudana a Abuja ya samun halartar manyan jagororin jam’iyyun, wanda suka haɗa da Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, David Mark da Peter Obi. Sauran sun haɗa da Abubakar Malami; Babachir Lawal; Rotimi Amaechi; da kuma Sanata Aminu Tambuwal. Haka kuma, akwai Seyi Makinde; Kabiru Tanimu Turaki; Farfesa Jerry Gana; Adolphus Wabara; da kuma Babangida Aliyu. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke cigaba da zargin gwamnatin…
