10
Apr
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya sanar da soke duk wani alƙawarin bayar da biza, yana umartar masu neman aiki da su duba imel ɗinsu don ƙarin bayani akan ranakun da aka sake tsarawa. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Ofishin Jakadancin ya ce ayyukan biza za su cigaba a ofishin jakadancin Amurka da ke Legas. Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ba da izinin gaggawa ga ma'aikatan gwamnatin Amurka da danginsu su bar ofishin jakadancin da ke Abuja, yana mai ambaton taɓarɓarewar lamuran…
