
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rashin ganin Shugaba Bola Tinubu a wajen ƙaddamar da manyan ayyuka a Legas ranar Laraba ya ƙarfafa zargin rikici tsakaninsa da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar, duk da cewa gwamnatin jihar ta yi ƙememe wajen musanta hakan.
Duk da cewa an ruwaito cewa shugaban ƙasar yana Legas tun a ƙarshen mako, ba a gan shi ba a tarukan buɗe ayyana, inda ya bar Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya wakilce shi a wuraren.
Akan haka ne Akpabio ya jagoranci ƙaddamar da gadar Opebi zuwa Mende zuwa Ojota da babban ofishin hukumomi a Alausa, wanda aka sanya wa suna Bola Ahmed Tinubu Administrative Complex, waɗanda duka an shirya su cikin tsare-tsaren ziyarar aikin shugaban ƙasar.
Taron ya samu halartar manyan masu alfarma da suka haɗa da gwamnonin jam’iyyar APC domin ƙarfafa wa gwamnan nan Legas.
Daga cikinsu akwai Dapo Abiodun, Douye Diri, Babagana Zulum, da kuma Hope Uzodimma, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin APC.
Saidai, ba a iya gano ainihin dalilin da ya sa Shugaba Tinubu bai halarci taron ƙaddamar da ayyukan ba.
Da yake jawabi a taron, Akpabio ya bayyana cewa yana gudanar da aikin ne a madadin shugaba Tinubu, yana bayyana ayyukan a matsayin al’amuran bunƙasa ababen more rayuwa da hidimta wa jihar.
An gudanar da ayyukan ne a ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Sanwo-Olu waɗanda suka haɗa da gadar Ojota zuwa Opeb, Tolu Schools Complex a Ajegunle, filin wasa na Maracana Stadium da kuma ‘Lagos Food Logistics Hub’ a Abijo.
