Babaji

5689 Posts

Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Dawakin Kudu/Warawa daga Jihar Kano, Muhammad Ɗanjuma Hassan ya rasu bayan shafe shekaru 66 a duniya. Kakakinsa, Akin Rotimi ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a yau Asabar, inda ya ce ɗan majalisar ya rasu ne a jiya Juma’a, bayan fama da wan irashin lafiya na tsawon lokaci. Ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga majalisar dokokin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, yana mai faɗin irin gudunmawar da ya bai wa ci-gaban majalisa na tsawon shekaru. A cewarsa, tuni Kakakin…
Read More

Yadda makircin tsohon mataimakina na tsige ni ya yi rashin nasara – Gwamna Abba

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi yunƙurin cire shi daga mulki domin ya karbi kujerarsa. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin wasu mawaka (Mawallafan Abba Gida Gida) a gidan gwamnati da ke Kano. Rahotanni sun nuna cewa Gwarzo ya ajiye mukaminsa ne a lokacin da majalisar dokokin jihar ke shirin tsige shi, amma daga baya majalisar ta janye shirin tsige shi bayan murabus din nasa. Gwamna Yusuf ya ce har yanzu bai ga takardar murabus din tsohon mataimakin nasa ba, yana mai cewa babu wanda ya…
Read More

2027: Babu damar tsaya wa takara ga ‘yan siyasar da suka haura shekaru 55 a ADC – Nafi’u

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban tsagi na jam'iyyar ADC ya sanar da cewa jam'iyar ba za ta bar waɗanda shekarunsu ya haura 55 tsaya wa takara a ƙarƙashinta ba a babban zaɓen 2027 da ke tafe. Da yake ganawa da BBC Hausa, kamar yadda Blueprint ta ɗauko, Nafi'u Bala ya bayyana cewa tsarin wanda ake shirin tabbatarwa na da nufin bai wa matasan 'yan siyasa a Nijeriya damar faɗaɗa harkokinsu na jagoranci. Ya kuma soki yadda 'yan siyasar da shekarun su ja ke tururuwar shiga jam'iyyar, inda yake cewa yanzu lokaci ne da ya dace a bai wa…
Read More

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ta jinjina wa Gwamnan Zamfara kan shimfiɗa ayyukan ci-gaba

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana cewa Jihar Zamfara yanzu ta zama mai sauƙin isa ga masu zuba jari da abokan hulɗa, tare da jaddada cewa majalisar na shirye ta zama abokiyar hulɗa wajen bunƙasa jihar. Amina Mohammed ta yi wannan bayani ne yayin wata ziyarar aiki da ta kai jihar Zamfara a ranar Alhamis, inda ta jagoranci tawagar manyan jami’an MDD domin duba halin da ake ciki a fannoni daban-daban. Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce Mataimakiyar Babban Sakataren ta kai ziyarar gani da ido a…
Read More

ECOWAS ta buɗe shafin ɗaukar ma’aikata na 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma Masu Tattalin Arziƙi (ECOWAS), ta buɗe shafinta na yanar gizo domin ɗaukar aiki na 2026, inda ta bayar da damar samun aiki ga masu sha'awar aiki da ita a ƙasashen ciki har da Nijeriya. A wani saƙo da ta fitar a ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce ɗaukar aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi wajen ƙarfafa ayyukanta da inganta su ta fannoni da dama. Da dama daga cikin guraben ayyukan galibinsu na a Abuja suke, inda ECOWAS take da ƙarfi. Daga cikin fannonin guraben akwai gudanarwa, lafiya,…
Read More

Jarumin ‘Game of Thrones’, Michael Patrick ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jarumin finafinan ƙasar Ireland wanda ya shahara da fim ɗin Game of Thrones, Michael Patrick ya rashu bayan shafe shekaru 35 a duniya sakamakon fama da rashin lafiya na tsawon lokaci. Matarsa, Naomi Sheehan ce ta tabbatar da mutuwarsa inda ta ce ya jima yana fama da cutar shanyewar ɓarin jiki tun tsawon shekaru uku da suka gabata. Ta bayyana cewa, mijin nata ya kasance jigo ne ga mutane da dama da ya haɗu su a lokacin da yake raye. A cewarta, ya samu shaidar zama mai ƙoƙarin ƙarfafa gwiwa ga masu ƙoƙarin tasowa…
Read More

Paparoma Leo zai zo Afirka yayin fara ziyarar ƙasashen duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Paparoma Leo na 14 zai fara ziyartar ƙasashen duniya da yankin Afirka a ranar Litinin, inda zai je Aljeriya, Kamaru, Angola da kuma Equatorial Guinea. Aƙalla zai shafe kwanaki 11 yana ziyarce-ziyarcen nasa waɗanda za su ɗauki tsawon sama da kilomita 18,000. Zai mayar da hankali ne akan tattaunawa tsakanin addinai, warware matsalolin rikici, rashin daidaito da 'yancin ɗan-adam a shiyyar. Ana sa ran zai gabatar da jawabi guda 11 a cibiyoyin al'umma da zai kai wa ziyara gabanin kammala balaguron nasa a ranar 23 ga watan Afrilu. Wannan na zuwa ne a daidai…
Read More

An yi jana’izar Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi a Zuru

An yi jana'izar gawar marigayi Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Muhammad Usman Zuru, a garin Zuru bayan gudanar da sallar jana’iza a Babban Masallacin Zuru a wannan Alhamis. Marigayin ya rasu ne a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, 2026, a wani asibiti da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar inda yake karɓar magani sakamakon jinya mai tsawo. An haifi marigayin a ranar 5 ga watan Afrilu, 1970, kuma ya bar mata guda da ’ya’ya biyar. A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana alhininsa kan rasuwar, inda ya ce jihar ta yi rashin babban jigo,…
Read More

Borno: Boko Haram ta fitar da bidiyon ‘yan Ngoshe 416 da ta yi garkuwa da su

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsagin Jama'atu Ahlis-Sunna Lidda'Awati Wal-Jihad da aka fi sani da Boko Haram, ya fitar da bidiyon da ke nuna halin da mutane 416 da suka sace a Ngoshe, wani ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno ke ciki sama da wata guda da harin yankin. A faifan na tsawon minti shida da daƙiƙu 43 da aka fitar a ranar Alhamis ƙungiyar ta nuna yare fa yin hira da mutanen, waɗanda galibinsu mata ne da yara da maza kaɗan acikinsu. An ga yadda suke roƙon gwamnatin Nijeriya da ta amince da buƙatun 'yan…
Read More

Ku haɗa kai ku kawo Kofin Duniya Afirka – Shugaban CAf ga Senegal da Moroko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), Dakta Patrice Motsepe, ya gana da jami'an ƙwallon ƙafa na ƙasar Moroko domin magance matsalolin rikicin Kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON). Motsepe ya tabbatar da cewa CAf tana shirye-shiryen yin gyare-gyaren ga dokokin tsare-tsaren AFCON da kuma sanya hukunci mai tsauri domin kauce wa irin rashin ɗa'ar da ya faru a wasan ƙarshe na gasar a aka yi a Junairu. Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da kwamitin ɗaukaka ƙara na CAf ya yi na ƙwace kofin daga hannun Senegal da ts yi nasara a wasan da…
Read More