
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Paparoma Leo na 14 zai fara ziyartar ƙasashen duniya da yankin Afirka a ranar Litinin, inda zai je Aljeriya, Kamaru, Angola da kuma Equatorial Guinea.
Aƙalla zai shafe kwanaki 11 yana ziyarce-ziyarcen nasa waɗanda za su ɗauki tsawon sama da kilomita 18,000. Zai mayar da hankali ne akan tattaunawa tsakanin addinai, warware matsalolin rikici, rashin daidaito da ‘yancin ɗan-adam a shiyyar.
Ana sa ran zai gabatar da jawabi guda 11 a cibiyoyin al’umma da zai kai wa ziyara gabanin kammala balaguron nasa a ranar 23 ga watan Afrilu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara rashin tabbas game da halin tsaro a sassan ƙasashen duniy, inda musamman saƙonni babban jagoran Kiristocin su shafi fannin addini da siyasa.
