
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jarumin finafinan ƙasar Ireland wanda ya shahara da fim ɗin Game of Thrones, Michael Patrick ya rashu bayan shafe shekaru 35 a duniya sakamakon fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Matarsa, Naomi Sheehan ce ta tabbatar da mutuwarsa inda ta ce ya jima yana fama da cutar shanyewar ɓarin jiki tun tsawon shekaru uku da suka gabata.
Ta bayyana cewa, mijin nata ya kasance jigo ne ga mutane da dama da ya haɗu su a lokacin da yake raye.
A cewarta, ya samu shaidar zama mai ƙoƙarin ƙarfafa gwiwa ga masu ƙoƙarin tasowa bisa sadaukarwa.
Haka kuma, ta bayyana takaicin rashinsa, inda ta ce hakan ya jefa iyalansa cikin jimami da ƙunci mara misali.
Rashin wannan jarumi ya sanya iyalai, abokai da magoya bayan mamacin cikin alhini musamman ganin yadda ya kasance zaƙaƙuri a waje da harkar fim.
