ECOWAS ta buɗe shafin ɗaukar ma’aikata na 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma Masu Tattalin Arziƙi (ECOWAS), ta buɗe shafinta na yanar gizo domin ɗaukar aiki na 2026, inda ta bayar da damar samun aiki ga masu sha’awar aiki da ita a ƙasashen ciki har da Nijeriya.

A wani saƙo da ta fitar a ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce ɗaukar aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi wajen ƙarfafa ayyukanta da inganta su ta fannoni da dama.

Da dama daga cikin guraben ayyukan galibinsu na a Abuja suke, inda ECOWAS take da ƙarfi.

Daga cikin fannonin guraben akwai gudanarwa, lafiya, kuɗi, shari’a da kuma tuntuɓa akan lamuran siyasa.

Guraben sune: “Office Aide, Programme Assistant, Nurse, Protocol Assistant, Documentation and Archives Assistant, Office Manager, accounting roles, Legal Officers, Political Adviser, as well as senior positions such as Principal Officers and departmental heads”, kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito.

Haka kuma, ECOWAS ta ce akwai guraben jami’an gudanarwa da harkokin kuɗi a Addis Ababa, tsare-tsaren wasanni a Laberiya, and babban kula da shirye-shirye musamman akan ruwa da kula da muhalli a Conakry.

Sannan, akwai guraben jami’an shari’a da gudanarwa a Dakar da wasu birane.

Ta shawarci masu sha’awar aiki da ita da su ziyarci sahihin shafinta na yanar gizo domin cike sharuɗɗa da ƙa’idojin da ta gindaya domin tantancewa.

Za a kammala karɓar takardu da bayanan buƙatar neman aikin a ranar 30 ga watan Afrilu, 2026.

By Babaji