Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Matan gwamnonin Arewa sun gudanar da taronsu na farko na kwata-kwata a ranar 10 ga Afrilu, 2026, a fadar gwamnatin Jihar Zamfara.
Taron, wanda Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, uwargidan gwamnan Jihar Gombe ta jagoranta, ya tattaro matan gwamnonin Arewa domin tattauna shirye-shiryen da aka tsara don inganta walwalar mata, yara, da kuma ƙungiyoyi masu rauni.
Wani ɓangare na shawarwarin da aka cimma a ƙarshen taronsu a cikin wata sanarwa ya haɗa da, Ci gaba da aikin haƙa rijiyoyin burtsatse don magance ƙalubalen matsalar ruwan sha tsaftatattce, ƙaddamar da sabin ayyukan tallafawa alumma a 2026.
Sauran ƙudurin sune, sun aminta da a riƙa yin bikin ranar agaji ta duniya a ranar 5 ga Satumba kowace shekara, da kuma yin tarurruka na gaba duk bayan watanni huɗu, tare da aiwatar da taron na gaba a watan Yuli ko Agusta 2026.
Haka zalika sun jajjada ƙudurin su na jajircewa wajen kawo sauyi mai kyau da inganta rayuwar al’umma musamman mata da ƙananan yara da kuma masu ƙaramin ƙarfi a yankin na Arewacin ƙasar nan baki ɗaya.
