Daga USMAN KAROFI
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da ɗage aikin sabunta bayanan masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasar nan zuwa bayan kammala zaɓen gama gari na shekarar 2027.
Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin wata takarda da kwamishinan ƙasa kuma ahugaban kwamitin yaɗa labarai da Ilimantar da masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, an cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da hukumar ta gudanar tare da Kwamishinonin zaɓe na Jihohi (RECs) a ranar 10 ga Afrilu, 2026, inda aka tattauna batutuwan zaɓe ciki har da wannan shiri.
INEC ta bayyana cewa aikin sabunta bayanan masu zaɓe na daga cikin muhimman ayyukanta na tabbatar da ingantaccen rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta ƙasa. An tsara aikin ne domin tantance bayanai, cire sunaye masu maimaituwa ko marasa cancanta, tare da ƙarfafa sahihancin kundin rajistar masu zaɓe.
Haka kuma, aikin na bai wa masu zaɓe damar tabbatarwa da gyara bayanansu idan akwai kuskure.
Sai dai duk da ɗage wannan shiri, INEC ta jaddada ƙudurinta na gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci, sahihanci da kuma haɗin kai a Najeriya.
