12
Apr
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma da dama sun hallara yayin da aka yi jana'izar mahaifin Babban Daraktan Kudi da Asusu na Jaridar Blueprint a garin Ososa da ke Ƙaramar Hukumar Odogbolu ta Jihar Ogun. Tun a ranar Juma'a ne aka fara hidimar domin karrama marigayin mai suna Pa Samson Idowu Oletubo, wanda ya rasu a ranar 13 ga watan Fabarairu bayan shafe shekaru 92 a duniya. An ga yadda aka samu cinkoson ababen hawa ) a yankin da ba a saba gani duba da yadda ɗimbin jama'a suka halarci jana'izar. Haka kuma gidan marigayin ya gaza ɗaukar adadin…
