Babaji

5689 Posts

Taron ADC na fuskantar rashin tabbas bisa zargin matsin lamba kan mai wurin taron

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban taron jam'iyyar ADC da aka shirya ya shiga halin rashin tabbas sa'o'i gabanin fara gudanarwa, bayan waɗansu zarge-zarge da jam'iyyar ta yi akan cewa akwai yunƙurin hana ta amfani da wurin taron da ta karɓa duk da cewa ta ƙulla yarjejeniya da mai shi da kuma biyan cikakken kuɗin da aka buƙata. A wata sanarwa da aka aike wa manema labarai, ADC ta zargi mai wurin da fuskantar matsin lamba na ya janye yarjejeniyar da ya ƙulla da jam'iyyar don haddasa tsaiko ga taron. A cewar jam'iyyar, hukumar gudanarwar Rainbow Event Centre ta…
Read More

Trump ya wallafa hotonsa a matsayin Annabi Isa yayin martani ga Paparoma kan kiran tsagaita wutar yaƙin Iran

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki shugaban ɗariƙar katolita na duniya Fafaroma Leo, inda ya zarge shi da rauni wajen yaƙi da laifuka da kuma rashin ƙwarewa a harkokin ƙasashen waje. Da yake magana da manema labarai bayan wallafa saƙon a shafukan sada zumunta, Trump ya ce shi ba “babban mai goyon bayan” Fafaroma ba ne, wanda ya yi ta bayyana ra’ayoyinsa kan yaƙin Amurka da Isra’ila ke yi da Iran. A nasa ɓangaren, Fafaroma Leo ya bayyana barazanar da shugaban ya yi ta rusa al'umma da tarihin Iraniyawa a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba”.…
Read More

‘Tun da jimawa mutane suka bar ƙauyen’: Sojoji sun yi ƙarin haske kan harin da shaidu suka ce ya halaka sama da mutane 56

Rundunar sojin Nijeriya ta kare harin jirgin sama da aka kai kasuwar Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe, inda aka ce mutane da dama sun rasu tare da jikkata. Jaridar TheCable ta rawaito cewa, gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa harin ya gudana ne yayin wani farmakin da aka kaddamar kan wadanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a yankin. Sai dai kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin, tana zargin cewa sama da mutane 100 ne suka mutu. A wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Sani Uba, ya…
Read More

Sojoji sun kama ɗan shekara 15 da aka danganta da kisan birgediya janar a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai sun yi ram da wani matashi mai kimanin shekaru 15 bisa zargin sa da hannu a kisan wani mummunan hari da aka kai a Jihar Borno. Matashin mai suna Tijjani Madu ya shiga hannun jami'an tsarin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa siyo abinci ga sauran 'yan uwansa 'yan ta'adda. Wata majiya mai ƙarfi ta ce, ana zargin sa da hannu a harin da ya yi sanadiyyar mutuwar Birgediya Janar Oseni Braimah da wasu dakaru da dama. A ranar Alhamis aka ƙaddamar da harin a…
Read More

Amurka ta jinjina wa gwamnatin Nijeriya kan hukunci ga ‘yan ta’adda 386

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Amurka ta yaba wa Nijeriya bisa hanzarta aiwatar da shari’o’in da suka shafi ta’addanci a ƙasar, bayan an yanke hukunci akan mutane 386 da ake zargi da hannu a ayyukan. A wata sanarwa daga babban mai bada shawara na Amurka akan harkokin Afirka da Larabawa, Massad Boulos ya fitar, ya ce wannan mataki na nuna ƙoƙarin ƙarfafa adalci da riƙon amana a tsarin shari’a, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Ya jaddada cewa gudanar da shari’a cikin gaggawa da gaskiya na da muhimmanci wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da kuma tabbatar da tsaron ƙasa.…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kanal na soja da wasu dakarun tsaro sun rasu a sabon harin Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mayaƙan Boko Haram sun halaka Kanal I.A. Muhammad na Rundunar Sojin Nijeriya da wasu sojoji da dama a yayin wani hari da suka kai cikin dare a wani sansanin sojoji da ke Monguno a Jihar Borno. A daren ranar Lahadi wayewar Litinin ne maharan suka kai farmakin akan Forward Operating Bas (FOB) da ke ƙarƙashin Bataliya ta 242 a Mungunu, wanda ya sauka akan sashe na 3 na ayyukan atisayen sojoji yayin aikin daƙile ta'addanci. Wasu sojoji da aka tura fage fama a yankin Arewa ta Gabas sun bayyana wa ShaharaReporters a yau Litinin…
Read More

Zamfara: Gwamnan Zamfara ya yi jimamin kisan gilla a Bukkuyum

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana matuƙar alhini da jimami akan munanan hare-hare da ’yan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum da ke jihar waɗanda suka yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama da raunata wasu. Gwamnan ya bayyana harin da aka kai da dare a ƙauyukan Bunkasau, Yar Galma (Unguwar Zarumai) da kuma Dogon Daji (Unguwar Adabka) a matsayin mummunan aiki na tashin hankali da rashin tausayi, wanda aka aikata akan fararen hula bisa rashin imani. A wata takarda da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, Gwamnan ya…
Read More

Yobe: Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

Wani mummunan lamari ya auku a kan iyakar Jihar Borno da Jihar Yobe, inda rahotanni ke cewa wani hari daga sama da sojoji suka kai ya fada kan wata kasuwa ta al’umma, lamarin da ake fargabar ya hallaka fiye da mutane 50. Bisa ga bayanan da ke fitowa a hankali, an ce harin ya faru ne yayin wani samame da ake kai wa ‘yan tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabas. Sai dai abin takaici, fararen hula sun tsinci kansu a cikin harin, wanda ya jawo asarar rayuka da raunuka masu yawa Rahotanni masu ƙarfi na nuna cewa lamarin…
Read More

Trump ya umarci sojin ruwan Amurka ta karɓe iko da mashigar Hormuz bayan tattaunawar tsagaita wuta ta rushe

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya umarci rundunar ruwan sojin Amurka da ta fara mamaye mashigar ruwan Strait of Hormuz nan take, bayan da tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe. Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar zaman lafiya da aka yi tsakanin kasashen biyu ba ta kai ga cimma matsaya ba, musamman kan batun shirin nukiliyar Iran. Trump ya ce rundunar ruwan Amurka za ta dakatar da duk wani jirgin ruwa da ke shiga ko fita daga mashigar, tare da hana duk wanda ya biya kudin wucewa ga Iran samun kariya. Wannan mataki na iya kara tsananta rikici a…
Read More

Bayan wata biyar, ɓangaren Wike na PDP ya karɓe iko da sakatariyar jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bayan watanni biyar da rufe sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Wuse Zone 5 a Abuja akan rikicin jagoranci, hukumar 'yan sandan Nijeriya ta buɗe shi. An damƙa sakatariyar da ke Wadata Plaza ga tsagin Ministan Abuja Nyesom Wike, ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, wanda shi ne sabon zaɓaɓɓen shugaban jam'iyyar na ƙasa. Tun a watan Nuwamba ne aka garƙame ofishin akan rikicin shugabanci tsakanin tsagin su Tanimu Turaki (SAN) da kuma kwamitin kula da jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed. A yanzu dai rundunar 'yan sanda ta bayar da damar cigaba da amfani da ofishin, wanda…
Read More