
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana matuƙar alhini da jimami akan munanan hare-hare da ’yan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum da ke jihar waɗanda suka yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama da raunata wasu.
Gwamnan ya bayyana harin da aka kai da dare a ƙauyukan Bunkasau, Yar Galma (Unguwar Zarumai) da kuma Dogon Daji (Unguwar Adabka) a matsayin mummunan aiki na tashin hankali da rashin tausayi, wanda aka aikata akan fararen hula bisa rashin imani.
A wata takarda da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu, yana mai nuna alhini da jimami tare da su a wannan lokaci na babban rashi da baƙin ciki.
Akan haka ne ya umarci a tura wata babbar tawaga ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna domin kai saƙon jaje, tallafa wa iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka jikkata sun samu kulawar lafiya cikin gaggawa.
Kazalika, “ya tabbatar wa al’ummar jihar Zamfara cewa gwamnatinsa za ta ƙara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da ɗaukar matakai masu ƙarfi domin dawo da zaman lafiya a dukkan sassan jihar,” kamar yadda mai magana da yawun nasa ya bayyana.
