AIG Bello ya bada umarnin murƙushe ‘yan bindiga a Kaduna da Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, mai kula da shiyya ta huɗu dake kula da jihohin Kaduna da Katsina, wadda ke da helkwata a Katsina a karƙashin jagorancin AIG Bello Shehu ta umurci kwamishinonin ‘yan sandan jihohin Kaduna da Katsina da su ƙara ɗaukar matakan sabbin dabarun da za su murƙushe hare-haren ‘yan bindiga da kuma sauran laifuffuka.

Bayanin hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na ofishin mataimakin sufeto janar mai kula da shiyya ta sha huɗu dake Katsina, ASP Umar Muhammad ya sanya wa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan umurnin ya fito a ƙoƙarin babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu na ganin an kawo ƙarshen matsalolin tsaro musamman na ‘yan bindiga da sauran laifuffuka a wannan shiyyar da ma ƙasa baki ɗaya.

AIG Bello Shehu ya kuma umurci kwamishinonin yan sandan jihohin Kaduna da Katsina da su ƙara tura zaratan haziƙan ‘yan sanda na musamman domin daƙile duk wani yunƙurin ɓatagari a garuruwan da ake fama da matsalar tsaro a jihohin.

Haka kuma ya shawarci kwamishinonin ‘yan sandan su dinga yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami’an tsaro da ake aiki tare wajen ganin sun magance ta’addanci a jihohin.

AIG Bello Shehu ya yi kira ga al’umma su cigaba da ba da guddumuwarsu ta hanyar taimaka wa da bayanan sirri ga jami’an tsaro na maɓoyar miyagun mutane a yankunan su domin ɗaukan mataki.

By ukarofi