16
Apr
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba aka yi jana'izar Birgediya Janar Omo Braimo, Kyaftin Ismail da wasu dakarun tsaro da suka rasu a yayin yaƙi da ta'addanci a Nijeriya. Taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da jami'an sojoji daga matakin jiha da kuma ƙasa. An yi jana'izar ne a maƙabartar sojoji ta Maimalari da ke Maiduguri, inda aka samu halartar masu jimami daga sassan Nijeriya daban-daban domin jinjina wa sadaukarwar da dakarun suka yi a bakin aiki. Daga cikin waɗanda suka je taron akwai Gwamna Umara Babagana Zulum na Jihar Borno; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa;…
