Babaji

5689 Posts

Kaduna, Bauchi da jihohi tara sun karɓi biliyan N44 na kuɗin UBEC bayan rahoto

Hukumar kula da lamuran ilimi a matakin Farko ta Ƙasa (UBEC) ta fitar da jimillar Naira biliyan 44.24 a matsayin kuɗaɗen tallafin daidaito ga jihohi 11. Rahotanni sun bayyana cewa, jaddawalin raba kuɗin da aka wallafa a shafin UBEC ya nuna cewa jihohin da suka karɓa sun haɗa da Jigawa, Ondo, Taraba, Kogi, Kaduna, Filato, Osun, Zamfara, Bauchi, Sakkwato da Inugu. An tsara wannan tallafin ne domin taimaka wa kowace jiha da kuma Babban Birnin Tarayya , don samar da muhimman gine gine da ake buƙata wajen aiwatar da shirin Ilimi a matakin Farko na Ƙasa (UBE). Ana ƙididdige rabon…
Read More

2027: Burin Atiku na tsaya wa takara shure-shure ne da baya hana mutuwa, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana burin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar na tsaya wa takara a 2027 a matsayin shure-shuren da baya hana mutuwa bayan wani rashin kataɓus a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin. Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan harkar yaɗa labarai, Suday Dare ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce hirar da aka yi da Atiku ta nuna rashin hangen nesa da shirin shugabanci a matakin ƙasa daga tsohon mataimakin shugaban ƙasar. A cewarsa,…
Read More

Abin da ya sa MTN ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya dakatar da tsarin bayar da bashin katin kira da data bayan gabatar da sabuwar buƙata da Hukumar kula da Gasa da Bada Kariya ga Kwastomomi (FCCPC) ta yi, wanda ke nuna an samu takura na bayar da rance a fagen dijital a ƙasar. Rahotanni sun bayyana cewa babban kamfanin sadarwar ya bayyana haka ne a wata takarda da ya miƙa wa Kamfanin Canji na Ƙasa a ranar Alhamis, inda ya ce an dakatar da tsarin ne na wucin-gadi wanda ya zama wajibi sakamakon tabbatar da bin dokokin…
Read More

Yaƙin Gabas ta Tsakiya: Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na kwana 10 a Lebanon

Gwamnatin Lebanon ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta kwanaki 10, domin samun damar tattaunawa don samar da cikakkiyar yarjejeniya ta dindindin. A farkon makon nan wakilan gwamnatin Lebanon da Isra'ila suka halarci Washington domin tattaunawa ta kai tsaye, inda suka gana da Shugaban Amurka, Donald Trump a fadar White House. Bayan ganawar, Trump ya sanar da tsagaita wutar tsakanin bangarorin biyu, wanda ya ce za ta fara aiki da ƙarfe 5 na Yamma (agogon Amurka), kuma za ta ɗauki kwanaki 10. Saidai ƙungiyar Hezbollah ta ce ba ta cikin yarjejeniyar da aka cimma, kuma za ta cigaba da…
Read More

Likita ta rasu bayan haihuwar ‘yan uku a Bayelsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata likita mai suna Dakta Ere Ogbachi, ta rasa ranta a Jihar Bayelsa bayan ta haifi ’yan uku, sakamakon matsalolin lafiya da suka taso mata bayan faruwar al'amarin. Bayan haihuwar jariran a Asibitin koyarwa na jami’ar Neja-Delta da ke Okolobiri, rahotonni sun ce halin lafiyar likitar ya shiga matsanancin yanayi, wanda ya sa aka gaggauta kai ta sashin kulawa na musamman (ICU) na Babban Asibitin Tarayya da ke Yenagoa, babban birnin jihar. Wani ɗan uwanta mai suna Meshack Sintei, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceto ranta, ta rasu…
Read More

Kotu ta bada umarnin kama tsohuwar Ministar Jin ƙai Sadiya Umar Farouk da Nura Alƙali

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Alƙali Jude Onwuegbuzie ta bayar da izinin kama tsohuwar Ministar Jin ƙai, Sadiya Umar Farouq, da tsohon Babban Sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alƙali bisa zargin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe. Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, na tuhumar su da laifuka guda 21, waɗanda suka haɗa da cin amanar aiki da karkatar da kimanin dala miliyan 1.3 da kuma sama da Naira miliyan 746.5 a lokacin da suke riƙe da muƙaman. Saidai, yayin da aka nemi su gurfanar a kotu, ba su halarta ba,…
Read More

Rundunar ‘yan sanda ta damƙa wanda ake zargi da safarar hodar iblis ga Birtaniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta miƙa wanda ake zargi da hannu a manyan laifuka mai suna Mathew Chukwuemeka Adebiyi ga ƙasar Birtaniya domin ya fuskanci gurfanarwa akan zarge-zargen kisa da safarar miyagun ƙwayoyi. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Anthony Okon Placid ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis ta sahihin shafin hukumar na dandalin Facebook. A cewar sanarwar, an gudanar da haka ne ta Cibiyar ayyukan hukumar ta kula da lamuran ƙasa-da-ƙasa (NCB) a Abuja, bayan buƙatar da hukumomin Ingila suka miƙa a watan Satumbar 2024. Hukumomin 'yan…
Read More

NAHCON ta gargaɗi maniyyata akan wakilan bizar ƙarya, ta ce Saudiyya ta rufe bayarwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta aike da saƙon gargaɗi game da damfara da wakilan tafiye-tafiye da shafukan sada zumunta na bogi ke yi, waɗanda ake zargin su da iƙirarin samar da bizar zuwa aikin hajji duk da cewa ƙasar Saudiyya ta rufe bayarwa a hukumance. A cewar NAHCON, hukumomin Saudiyya sun rufe aikin bayar da biza tun a ranar 1 ga watan Shawwal, 1447, wato 20 ga Maris, 2026, lamarin da ke nuna kawo ƙarshen aikin neman biza ga maniyyatan bana. Hukumar ta kuma sanar da cewa, tun gabanin wa'adin rufewar ya cika,…
Read More

Hajjin 2026: Saudiyya ta rage adadin mahajjatan Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Saudiyya ta sanar da rage adadin mahajjatan da ta ware wa Nijeriya, wanda hakan ya tilasta wa hukumar jigilar alhazan Jihar Zamfara rage maniyyata guda 456 daga shiga sahun waɗanda za su je aikin hajji a 2026. Shugaban hukumar, Musa Mallaha ya bayyana haka a wata hira da 'yan jarida a Gusau, inda ya ce ragin ya sa aka zaftare wa Zamfara adadi daga 2,207 zuwa 1,741. Saidai duk da haka, hukumar ta ce tana cigaba da shirye-shiryen aikin hajjin na bana, inda nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar ta za fara jigilar…
Read More

CAC ta tabbatar da kutse a matattarar bayananta, ta shawarci jama’a su kula

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da harkokin kasuwanci da masana'antu (CAC) ta bayyana cewa tana gyara akan wani al'amarin tsaron sashen yanar gizonta da ya fuskanci kutse a wani sashe na matattarar bayananta. A wata sanarwa da aike wa manema labarai a ranar Laraba, hukumar ta ce kutsen ya shafi wani ƙaramin sashi ne na matattarar, inda ta ce tuni ta ɗauki matakin gaggawa yayin da ta gano al'amarin. CAC ta kuma ce tana aiki da Hukumar Ci-gaban Fasahar Sadarwa (NITDA) tare da wasu hukumomin gwamnati da wasu ɓangarori domin gano mataki da tasirin al'amarin. A cewarta,…
Read More