Neja: Mutane biyar sun rasu yayin da aka ƙone gidaje a sabon harin ‘yan bindiga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gidaje da dama sun ƙone yayin da wasu ‘yan bindiga suka halaka mutane biyar da yin awon-gaba da wasu da dama a ƙauyen Baga da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki yankin ne da safiyar ranar Talata, lamarin da ya tilasta wa jama’a tserewa da barin gidansu da aka ƙone a sanadiyyar haka.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewa sama da ‘yan bindiga guda 160 ne suka shiga ƙauyen inda suka yi ta amfani da ababen fashewa wajen lalata gidaje da wasu kadarorin al’umma.

Haka kuma, an ruwaito cewa aƙalla ‘yan bijilante takwas ne suka jikkata yayin ƙoƙarin mayar da martanin akan harin, saidai ƙarfin makaman maharan ya kere nasu.

A yanzu dai ana kula da waɗanda suka samu raunukan a wani asibiti.

Wasu majiyoyi sun ce a ranar Litinin ne maharan suka sace waɗansu dabbobi a kusa da Baga a yankin ƙauyen Nada na ƙaramar hukumar, wanda bayan nan ne suka kutsa zuwa Baga.

Tuni dai aka baza jami’an tsaro a yankin domin kwantar wa al’umma hankali da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya; saidai, babu wani rahoto na musamman akan al’amarin daga ‘yan sanda a lokacin haɗa wannan rahoto.

By Babaji