NYSC ta gargaɗi ‘yan hidimar ƙasa akan tafiyar dare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da harkokin ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta gargaɗi masu shirin fara hidima da su guji yin tafiye-tafiye a lokutan dare.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ta sanar da fara jigilar ‘yan rukunin A diba na 2, wanda za a fara a ilahirin jihohin Nijeriya.

Daraktar yaɗa labaran hukumar, Caroline Embu ta bayyana haka a wata takarda da fitar a yau Laraba a Abuja.

A cewar sanarwar, za a fara rajistar horon wayar da kan na sati uku ne ga sabbin ‘yan hidimar daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Afrilu, 2026.

Haka kuma, ta ce za a yi taron rantsarwa a ranar 24 ga wata, wanda ke nuna mafarin ayyukan wayar da kan a hukumance.

Ta ƙara da cewa, za ƙarƙare horon ne a ranar 12 ga watan Mayu, inda daga nan za a tura ‘yan hidimar zuwa wuraren da zu yi aikinsu a sassan jihohin da aka tura su.

Kazalika, ta shawarce su da su tsara tafiye-tafiyensu yadda ya dace domin isa sansanonin da aka tura su cikin ƙoshin lafiya da tsaro.

By Babaji