28
Mar
Babbar Kotun Tarayya a Jihar Jigawa ta dage hukunci a shari’ar Walida Abdulhadi, yarinya da ake zargin jami’in DSS ya sace kuma ya yi mata fyade, zuwa ranar 28 ga Afrilu, 2026. A baya, kotu ta riga ta dage sauraron shari’ar ranar 11 ga Maris don ba wa lauyan kare wanda ake tuhuma damar shirya takardun kare kansa a kan zargin Walida, ’yar ƙaramar hukumar Hadejia, da ya ɗauke a shekarar 2023. A zaman kotu da aka yi ta Zoom, lauya Abdulmalik Sani ya roki karin lokaci don shigar da takardun kare kansa, yana mai cewa suna bukatar karin bayanai.…
