Babaji

5689 Posts

Trump ya ci alwashin ƙaddamar da luguden wuta a Iran matuƙar ta bijire wa sulhu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce a shirye yake ya yi wa Iran luguden wuta matuƙar ta ƙi amince wa buƙatar tattaunawa akan tsagaita wutar yaƙin da ke tsakaninsu. A ranar Laraba ne Sakatariyar Fadar White House, Karoline Leavitt ta musanta batun da ke cewa an yi baran-baran a tattaunawar da Amurka ke yi da Iran. A cewar Leavitt, ana cigaba da tattaunawa kuka ana samun ci-gaba a kai, kamar yadda ta bayyana a wata hira da manema labarai. Ta ce, akwai ƙamshin gaskiya a game da rahotannin da ke cewa akwai ajanda…
Read More

Senegal ta shigar da ƙara a CAS bayan CAF ta ƙwace AFCON a hannunta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta ƙasar Senegal (FSF) ta shigar da ƙorafi ga Kotun Shari'o'in Wasanni (CAS) domin ta ƙalubalanci hukuncin Hukumar kula da Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) na ƙwace Kofin gasar ƙasashen Afirka (AFCON) daga gare ta. CAS ta tabbatar da haka a ranar Laraba inda ta ce an shigar da ƙorafin a hukuncin, wanda ke nuna cewa matakin ya soke rahotannin da ke nuna cewa hukumomin Senegal ba su miƙa ƙorafin nasu ba a lokacin da ya dace. Al'amarin ya samo asali ne a ranar 17 ga watan Maris,…
Read More

Birnin Gusau ya yi cikar kwari yayin da Shettima da gwamnoni 10 suka tarbi Gwamna Lawal zuwa APC

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranci gwamnonin jihohi goma tare da shugabannin jam’iyya wajen tarbar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zuwa jam’iyyar APC. An gudanar da wannan gagarumin taro ne a ranar Talata a filin kasuwanci na Trade Fair da ke Gusau, inda dubban magoya baya, ’yan Majalisar Dokoki, da mambobin Majalisar Zartarwa suka halarta domin shaida wannan lamari mai muhimmanci a siyasar jihar. Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa sabon filin jirgin saman Gusau na ƙasa da ƙasa, wanda aka kammala kwanan nan. Daga…
Read More

Mohamed Salah zai bar Liverpool a ƙarshen kakar bana

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga Birtaniya sun nuna cewa tauraron ɗan ƙwallon Misra, Mohamed Salah ya shirya barin ƙungiyar Liverpool bisa yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu. Liverpool ta bayyana hakan a shafinta na yanar gizo a ranar Talata, inda ta ce zaman Salah ƙungiyar zai zo ƙarshe a ƙarshen kakar 2025-2026. Wannan ya nuna cewa ɗan wasan ya amince da ficewa daga ƙungiyar bayan shekara tara yana wakiltar Liverpool a wasannin gasa da dama da take ciki. Salah a nasa ɓangaren, ya yi godiya ga magoya bayan ƙungiyar bisa damar da ya samu a Liverpool yayin da ya…
Read More

An kama malaman asibiti bisa yin allurar da ta yi ajalin ‘yan uwa biyu a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An kama malaman asibiti guda biyu bisa hannu a mutuwar wasu ƙananan yara mata biyu 'yan gida ɗaya bayan zargin ba su maganin da bai dace da rashin lafiyarsu ba a Babban Asibitin Gwamnati da ke Zuru a Jihar Kebbi. Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa masu shekaru shida da uku, sun rasu ne a ranar 18ga watan Maris, bisa zargin sakaci daga ɓangaren ba su magani a asibitin. A yanzu haka waɗanda ake zargi da laifin suna hannun hukumar 'yan sanda, inda ake gudanar da bincike akansu domin gano haƙiƙanin abin…
Read More

Binance na neman sulhu da Gwamnatin Tarayya kan shari’ar rashin biyan haraji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kamfanin Binance Holdings Limited da ya shahara da harkar cinikayar kuɗaɗen intanet (cryptocurrency), ya fara tattaunawa da hukumomin Nijeriya domin warware matsalolin shari'ar rashin biyan haraji akansa, matakin da ya dakatar da sauraron ƙarar batun da ke gaban Babbar Kotun Tarayya ta Abuja. An sanar da haka ne yayin da Mai Shari'a Emeka Nwite nemi a cigaba da sauraron shari’ar, inda ɓangarorin masu kare wanda ake ƙara da na masu gurfanarwa suka tabbatar wa kotun cewa an fara tattaunawa neman sulhu tsakanin kamfanin da kuma gwamnati. Lauyan da ke kare Binance, Sunday Agaji ya…
Read More

Kotu ta ɗage sauraron buƙatar ba da belin El-Rufa’i

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Kaduna, ta ɗage sauraron buƙatar belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga Maris, 2026. An ɗauki wannan matakin ne bayan zaman kotun na ranar Talata, inda ɓangaren masu ƙara da masu kare kai suka gabatar da hujjoji. A zaman kotun, lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci kotun da ta ba da belin tsohon gwamnan, yana mai cewa hakan na cikin haƙƙinsa a kundin tsarin mulki, tare da buƙatar samun isasshen lokaci domin shirya kare shi a kotu. Sai dai ɓangaren masu ƙara sun yi adawa da buƙatar, suna mai cewa…
Read More

Umarnin kotu muka bi ba samame ba, inji EFCC kan dirar mikiya gidan Malami na Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta bayyana hikimar da ta sanya jami'anta suka yi wa kadarorin tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami dirar mikiya, inda ta ce hakan yana ƙarƙashin doka da sahalewar umarnin kotu. EFCC ta ce, abin da mutane da dama suka bayyana a matsayin samame, wani ɓangare ne daga cikin ayyukan da hukumar ke yi da umarnin ƙwace kadarorin na wucin-gadi daga wata babbar kotu. Da yake magana a jiya Litinin, Kakakin EFCC Dele Oyewale, ya ce jami'an su kan sanya alamar bincike ne akan kadara don ankarar…
Read More

Jami’an tsaro sun kai samame gidan Malami na Abuja sa’o’i bayan ziyarar Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An sake shiga fargaba a ranar Litinin yayin da jami'an tsaro suka kai samame a gidan tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami da ke Abuja. Rahotanni sun bayyana cewar al'amarin ya faru ne sa'o'i kaɗan bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya kai masa ziyara a gidan nasa. A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, an ga yadda Malami yake ƙalubalantar jami’an tsaron kan sahihancin umarnin da suka zo da shi, yana mai cewa batun na gaban kotu kuma bai kamata a ɗauki wani mataki ba ba tare da umarni daga gare…
Read More

Kakaki da ‘yan majalisa 12 sun koma APC daga PDP a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Moriki, da wasu mambobin majalisar 12 sun bar jam'iyyar adawa ta PDP tare da koma wa mai mulki, APC. Hon. Moriki ya sanar da haka yayin zaman majalisar a jiya Litinin a Gusau bayan gabatar da takardun murabus ɗinsu ga majalisar. Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa matakin 'yan majalisar ya biyo bayan sauya sheƙar gwamnan jihar, Dauda Lawal ne daga PDP zuwa APC. A yau Talata ne ake sa ran karɓar gwamnan a APC a hukumance, kamar yadda Sakatariyar jam'iyyar ta Ƙasa ta bayyana. Taron…
Read More