23
Mar
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sanda ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Sufeto Janar na rundunar, Olatunji Disu ya umarci a rarraba dukkan sassan jami'anta da ke manyan ofisoshinta na jihohi. A wata sanarwa da ta aike wa 'yan jarida ta hannun Kakakinta Anthony Placid, rundunar 'yan sandan ta bayyana rahotannin a matsayin "rashin fahimtar haƙiƙanin abin da umarnin sufeton ya ƙunsa". A cewarta, wasu gidajen jarida sun yi ikirarin cewa sufeton ya umarci a gaggauta rarraba sassa jami'ai na musamman, wanda hakan ba shine abin da ake nufi ba. Ta bayyana cewa, Sufeto Janar…
