Babaji

5689 Posts

Shettima zai marabci Gwamnan Zamfara a APC ranar Talata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, zai ziyarci jihar Zamfara domin tarbar Gwamnan jihar, Dauda Lawal cikin jam’iyyar APC a ranar Talata mai zuwa. Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Tukur Ɗanfulani Maikatako ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Gusau ranar Asabar. Ya ce, mataimakin shugaban ƙasar tare da shugabannin jam’iyyar na ƙasa za su halarci taron domin ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓen shekarar 2027. Ya kuma kirayi mambobin jam'iyyar da ke gundumomi 147 na ƙananan hukumomi 14 da ke jihar da su fito ƙwansu da…
Read More

NATO ta janye dakarunta daga Iraƙi yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ƙamari

Kungiyar tsaron ƙasashen yammacin duniya ta NATO ta janye dakarunta daga aikin horaswa da ba da shawara a ƙasar Iraki, tare da mayar da su zuwa Turai, sakamakon tsananin rikicin yaƙin Iran da ke ƙara ƙamari. Rahotanni sun ce an kwashe dukkan jami’an NATO da ke cikin wannan aiki cikin tsaro, inda aka mayar da su zuwa wani hedikwata na soja a birnin Naples na ƙasar Italiya. Wannan mataki na zuwa ne yayin da rikicin yaƙi tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ke ƙara dagula al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya haifar da fargabar tsaro ga dakarun ƙasashen…
Read More

‘Yan bindiga sun sace sakataren ƙaramar hukuma a Kano

Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan sakataren Ƙaramar Hukumar Kibiya da ke Jihar Kano tare da sace shi. Shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Hon. Sabo Yusuf Usman ya shaida wa BBC cewa lamari ya faru ne ranar Juma'a da daddare a gidan sakataren da ke garin Dinya. ''Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da sakataren ke barci a gidansa'', in ji shi. Ya cigaba da cewa lokacin da maharan suka je gidan sun tashi ɗan gidan sakataren da ke kwana a zauren waje, inda suka tilasta masa ƙwanƙwasa kofar gidan, sannan ya faɗa wa…
Read More

Borno: Har yanzu akwai boma-boman ƙunar baƙin-wake biyu da ba su fashe ba, inji Gwamna Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu da ake zargin ‘yan ƙunar baƙin-waken guda biyu da ke yawo a cikin birnin Maiduguri bayan jerin fashe-fashe da suka girgiza babban birnin jihar. A wata hira da ya yi da BBC Pidgin a ranar Juma’a, Zulum ya ce rahotannin sirri na tsaro sun nuna cewa mutum biyar ne suka shigo cikin birnin da nufin kai hare-haren kunar bakin wake. Ya kara da cewa daga cikin wadannan mutane, wasu sun riga sun tayar da bama-baman su, yayin da sauran biyu har yanzu ba su aiwatar da nasu harin…
Read More

Guardiola ya caccaki CAF kan ƙwace AFCON a hannun Senegal

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana mamaki game da hukuncin Hukumar kula da Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) na ƙwace Kofin ƙasashen Nahiyar Afirka AFCON na 2025 da bai wa ƙasar Moroko, yana mai cewa an ɗauki matakin ne ba tare da adalci ba. Ya bayyana cewa, wannan matakin abu ne da aka ɗauka ta bayan fage, inda ya ce ya yi mamaki matuƙa a kai. Kwanaki biyu da suka gabata ne CAF ta sanar da ƙwace nasarar AFCON na 2025 daga hannun Senegal da bai wa Moroko bayan ƙorafi da hukumar ƙwallon…
Read More

Badaƙalar N400bn: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci a sake gurfanar da El-Rufa’i bayan soke hukuncin farko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙara a Kaduna, ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a shari’ar kare haƙƙin ɗan-adam da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya shigar. A hukuncin da alƙalai uku suka yanke a ranar 17 ga Maris, kotun ta ce an gudanar da shari’ar a matakin farko ne ba tare da cikakken adalci ba, wanda ya saɓa wa haƙƙinsa na samun sauraro na adalci, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Kwamitin alƙalan da suka yanke hukuncin ya haɗa da Onyekachi Otisi, Abimbola Obaseki-Adejumo, da Sybil Gbagi. Akan haka ne kotun ta…
Read More

Jarumin finafinan Amurka, Chuck Norris ya rasu bayan shekaru 86 a duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shahararren jarumin finafinan Amurka, Chuck Norris, ya rasu bayan shafe shekaru 86 a duniya. Marigayin ya shahara sosai a masana’antar finafinai saboda ƙwarewarsa a harkar faɗa da kuma rawar da ya taka a finafinai da dama na yankin Amurka. Mutuwarsa ta girgiza masoyansa da masu kallon fim a faɗin duniya, inda mutane da dama ke bayyana alhini da jimamin rashin sa. Za a ci lgaba da tunawa da shi saboda gudunmawar da ya bayar a harkar nishaɗi. Iyalansa sun bayyana cewa, "Cike da jimami muke sanar da kwatsam din rasuwar masoyinmu Chuck Norris a…
Read More

‘Yan sanda sun kama mai gari da wasu kan shirya bikin bajekolin fyaɗe

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Delta, ta kama wani jagoran al'umma kuma mai shirya wani taron al'ada a garin Ozoro mai suna Cif Omorede Sunday, tare da wasu mutane hudu, biyo bayan bayyanar wasu bidiyoyi da ke nuna cin zarafin mata da fyade a yankin Ƙaramar Hukumar Isoko ta Arewa da ke jihar. Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya bayyana a ranar Juma'a, 20 ga Maris, 2026, cewa hotunan bidiyon sun nuna yadda aka keta wa matasa mata haddi da mutunci, wanda hakan ya saba wa doka da hakkin ɗan-adam. Tuni dai Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aina Adesola ya bada…
Read More

Trump ya caccaki NATO kan ƙin taimaka wa Amurka a yaƙinta da Iran

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump na Amurka, ya caccaki ƙasashen mambobin ƙungiyar gamayyar tsaro ta NATO, inda ya bayyana su a matsayin matsorata sakamakon ƙin bayar da goyon baya ga Amurka da Isra'ila a yaƙinsu da ƙasar Iran. Wannan bayani na Trump na zuwa ne a lokacin da rikicin ke cigaba da durƙusar da tattalin arziƙin duniya, musamman ta fuskar tsadar kayayyakin makamashin man fetur da Iskar Gas saboda ƙamarin rikicin. Trump ya bayyana matuƙar ɓacin ransa akan yadda ƙasashen Turai suka ja da baya wajen tura dakarunsu ko bayar da tallafin soji, lamarin da ke…
Read More

Isra’ila kaɗai ke da alhakin kai hare-hare a tashar gas ɗin Iran, inji Netanyahu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fraministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa ce kaɗai taek da alhakin kai Faransa a tashar na ƙasar Iran yayin ake cigaba da shiga halin fargaba kan kai wa tashoshin makamashi hari a Gabas ta Tsakiya. Waɗannan hare-hare sun yi sanadiyyar tashin farashin dangogin makamashi, sannan Shugaba Donald Trump ya ce bai sanda su ba gabanin ƙaddamarwa. A wani labarin, Netanyahu ya ce ƙasarsa, ba za ta sake kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran ba. Yana magana ne bayan wani gargadi da shugaba Trumo ya yi masa kan sake yin hakan. Wani harin da…
Read More