
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya sauka a Legas domin bai wa Shugaba Bola Tinubu ba’asin matakin tsaro a Maiduguri, Jihar Borno, bayan ziyarar da ya kai a kwanan nan.
Ziyarar Shettima na zuwa ne bayan harin boma-boman ƙunar baƙin-wake a wasu wurare uku na Birnin Maiduguri da ya auku a ranar Litinin ɗin da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23 da raunata wasu sama da guda 100.
A wani saƙo da aka wallafa ta kafar X a yau Lahadi, Maitaimakin Shugaban Ƙasar ya ce ziyararsa ta zuwa Maiduguri an yi ta ne bisa umarnin Shugaba Tinubu domin ganawa tare da jajenta wa iyalai da yankunan da harin ya shafa.
A wannan ziyara ta Legas, ana sa ran Shettima zai yi wa Tinubu bayanin sakamakon rahoton zuwan nasa babban birnin Bornon.
A ranar Litinin da misalin ƙarfe 7:02 na yamma ne wasu ‘yan ƙunar baƙin-wake guda uku suka kai farmaki a sananniyar kasuwar Maiduguri da ake kira da Monday Market da yankin Post Office da kuma shingen binciken jami’an tsaro a mashigar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
A lokacin da ya ziyarci waɗanda jikkata a harin a asibitin ranar Laraba, Shettima ya yi alla-wadai da hare-haren, inda ya ce babu addinin da ya bayar da damar halaka waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.


