Babaji

5689 Posts

Florentino Perez ya tabbatar da kawo ƙarshen European Super League yayin da Real Madrid ta janye

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Real Madrid da Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Turai (UEFA) sun sanar da cimma yarjejeniya domin kawo ƙarshen rikicin sharri'o'i da ya biyo bayan rushewar gasar European Super League. Madrid, wadda shugabanta Florentino Perez ya daɗe yana goyon bayan gasar, tare da kamfanin A22 Sports Management, sun sanar da kawo ƙarshen shirin gasar European Super League a hukumance bayan an cimma yarjejeniya tsakanin UEFA, Kungiyoyin Kwallon Kafa na Turai (EFC), da kuma Real Madrid. An kirkiro tunanin Super League ne shekaru biyar da suka gabata tare da kungiyoyi kamar Real Madrid, Barcelona, Atlético…
Read More

Akwai yiwuwar hukuma ta kama ni a kowane lokaci – El-Rufa’i

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a kama shi a kowane lokaci daga ɓangaren hukumomin tsaron Nijeriya. El-Rufai, wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar BBCHausa a ranar Laraba, inda ya yi zargin cewa ana tilasta wa 'yan siyasa sauya sheƙa zuwa cikin jam'iyya mai mulki (APC). El-Rufa'i, wanda a baya-bayan nan ya kara matsawa wajen sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC da ya yi mulki a ƙarƙashinta na tsawon shekaru takwas, ya ce duk…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya naɗa Ambasada Isma’il Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya bayar da sunanan Ambasada Isma'il Abba Yusuf ga Majalisar Dattawa domin tantance shi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON). Wannan naɗi wani ɓangare ne na Sashe na 3(2) na kundin dokar NAHCON na 2026, inda aka miƙa buƙatar hakan a hukumance ga majalisar a jiya Talata ta wata wasiƙa daga Fadar Shugaban Ƙasa. A ciki Shugaba Tinubu ya nemi Shugaban majalisar,, Godswill Akpabio da ya jagoranci aikin tantancewa da tabbatar da Ambasada Abba Yusuf a muƙamin domin ba shi damar fara jagoranci ba tare da ɓata lokaci…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tottenham ta sallami koci Thomas Frank

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur, ta sallami mai horar da 'yan wasanta, Thomas Frank bayan shan kaye a hannun Newcastle United da ci 2 da 1 a ranar Talata. Frank, wanda ya karɓi ragamar jagorancin kulob ɗin a kakar bara bayan barin Brentford, ya bar Spurs a gurbi na 16 a teburin gasar Premier League, kuma maki biyar daga rukunin ƙungiyoyi uku da ke fuskantar barazanar fita a gasar a kaka ta gaba. Tottenham ta shiga halin tsaka-mai-wuya a 2026 bayan gaza yin nasara a koda wasa ɗaya ne daga cikin takwas da…
Read More

Majalisar Dattawa ta amince da watsa sakamakon zaɓe ta na’ura bayan ƙorafin ‘yan ƙasa

Majalisar Dattawa ta ce ta amince da aika sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na'ura a matsayin matakin farko na aika sakamakon, amma idan aka samu matsalar sadarwa, INEC za ta yi amfani da takarda a rubuce wajen aika sakamakon kamar yadda aka saba yi a baya. Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da ƙudirin a lokacin zaman gaggawa da majalisar ta yi akan dokar, yayin da shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya amince da ƙudirin bayan amincewar sauran 'yan majalisar. Daga nan ne majalisar ta kafa kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki da Majalisar Wakilai don tsefe dokokin kamar yadda tsarin…
Read More

DSS ta yi gargaɗin aukuwar wani hari a Kwara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, reshen jihar Kwara, ta aike wa Rundunar 'yan sandan jihar saƙon yiwuwar samun wani hari a Ƙauyen Gbabe na Ƙaramar Hukumar Baruten. Wannan gargaɗi na zuwa ne kwanaki kaɗan da 'yan ta'adda suka ƙaddamar da wani mummunan hari a Ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Hukumar Kaiama, inda suka halaka mutane da dama. A samu wani kwafin takardar ankararwar daga Daraktan DSS, J.S. Adams da ke ɗauke da kwanan wata kamar haka: 5 ga Fabrairu, 2026, inda a ciki aka nufaci Kwamishinan 'yan sandan yayin da ake tsaka…
Read More

Amurka ta tura wa Nijeriya sojoji 200 don yaƙar ta’addanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin sojoji guda 200 ne Amurka ta tura wa Nijeriya domin su bayar da horo ga dakarun tsaron Nijeriya wajen yaƙar 'yan ta'adda, kamar yadda wani rahoto da The Wall Street Journal ta wallafa ya nuna a ranar Talata. Wani sojan Amurka ya shaida wa jaridar cewa Amurka ta ɗauki matakin ne makonni kaɗan da Shugaba Donald Trump ya zargi Nijeriya da gaza ba al'ummar Kirista kariya daga hare-haren 'yan ta'adda. Rahoton ya kuma bayyana cewa, ana sa ran dakarun Amurkan za su tallafa wa ayyukan yaƙi da ta'addanci ta bada horo da kuma…
Read More

Kwana biyu da harin tirelolin wake, Boko Haram ta ƙwace na dabbobi a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne, sun ƙwace wasu tireloli guda huɗu da ke maƙare da dabbobi, inda suka yi awon-gaba da sama da shanu 100 a kusa da Kareto da ke Ƙaramar Hukumar Mobbar a Jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:25 na rana a ranar Litinin jim-kaɗan bayan manyan motocin sun bar yankin Damasak inda suka nufi Maiduguri, kamar yadda majiyoyin al'umma da na tsaro suka bayyana. Al'amarin na kwanan nan ya faru ne ƙasa da kwana biyu da mayaƙan suak cinna wa…
Read More

ADP ta caccaki Majalisar Dattawa kan sharuɗɗan miƙa sakamakon zaɓe ta na’ura

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar 'Action Democratic Party' ADP, ta bayyana damuwarta akan sabon gyaran dokar zaɓe da Majalisar Dattawa ta yi, wanda ya bada damar watsa sakamakon zaɓe ta hanyar na'ura, saidai bai mayar da hakan wajibi ba. Dokar ta kuma yi hukuncin yin amfani da takardar 'Form EC8A' a matsayin mafita matuƙar aka samu gazawar sadarwar intanet. A wata sanarwa da ADP ta fitar ta hannun Shugabanta na Ƙasa, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, jam'iyyar ta ce, duk da cewa janye matsayar farko da majalisar ta yi na ƙin amincewa da watsa sakamakon ta na'ura na nuna…
Read More

Farfesa Pakistan ya yi murabus a shugabancin NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Litinin Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa na shugabancin hukumar a hukumance. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, Farfesan ya ce ya ɗauki matakin ne bisa wasu dalilai na raɗin kansa da kuma shawarwarin da ya samu daga wasu daga cikin iyalansa. A cewarsa, bisa la'akari da sashe na 3(6) na dokokin NAHCON gyaran 2006, ya miƙa takardar yin murabus a hukumance ga Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR). A ranar Litinin ɗin ne wasu bayanai suka…
Read More