Babaji

5689 Posts

Haɓakar tattali za ta samar wa rayuwar kowane ɗan Nijeriya sauƙi, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira da gwamnoni 36 na faɗin Nijeriya tare da ministoci da sauran jami'an gwamnati da su yi aiki wajen ciyar da al'umma gaba da haɓakar tattali domin magance matsalolin 'yan Nijeriya na yau da kullum. Shettima ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin taron Majalisar Tattali ta Ƙasa (NEC) jim-kaɗan bayan jawabin Shugaba Bola Tinubu, wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. A cewarsa, hikimomin da wasu ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi suka yi amfani da su wajen ciyar da ƙasarsu da al'ummominsu…
Read More

Boko Haram ta aika saƙon barazanar hari ga wani ƙauye a Kwara bayan kisan mutane 162

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne da aka alaƙanta su da Ƙungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lidda'awatu wal-Jihad, sun aike da saƙo mai ƙunshe da barazanar kai hari ga mazauna Ƙauyen Dunshigogo da ke Ƙaramar Hukumar Kaiaman Jihar Kwara. A cewar rahoton ShaharaReporters, anyi zargin cewa an aika wasiƙar ne kai-tsaye zuwa ga 'yan ƙauyen, wadda a ciki aka yi gargaɗin cewa mayaƙan za su kai wa mutanen hari. Wannan ya yi kama da irin barazanar da aka yi ya 'yan ƙauyen Woro, inda aka halaka mutane 162 a wani mummunan hari da ya…
Read More

Ɗan sanda ya mayar da miliyan N2.6 da aka yi kuskuren tura wa asusun bankinsa a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani jami’in ɗan sanda mai muƙami kwanstabul, wato Mohammed Alhaji Muhammad, daga reshen rundunar na Jihar Borno, ya yi abin koyi inda ya mayar da kuɗi har Naira miliyan 2.6 da aka yi kuskuren tura masa ta asusun bankinsa. A lokacin da yake miƙa kuɗin ga asalin mai shi, Alhaji Muhammad ya bayyana cewa ba zai taɓa cin moriyar abin da ba nasa ba, domin tarbiyya da tsoron Allah ne suka koya masa hakan tun yana ƙarami. Ya ce, abin da ya ƙarfafa masa shi ne ƙoƙarin gyara mummunan fahimtar da wasu ke da…
Read More

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jaddada sahihancin dakatarwar Natasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta tabbatar da matakin Majalisar Dattawa na dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ta ce majalisar ta yi aiki ne hukuncin doka akan al'amarin. A hukuncin da alƙalai uku suka yanke a ƙarar da Natasha ta shigar akan Magatakardar Majalisar Dokoki Ƙasa da wasu mutum uku mai lamba CA/ABJ/CV/1107/2025, kotun ta ce dakatarwar ba ta tauye haƙƙin majalisa ko na kundin tsarin mulki da ya ba sanatar ba. Abin da kotun yi shine soke tuhumar raina kotu da kuma tarar Naira miliyan 5 da aka ƙaƙaba…
Read More

Kakan Mohamed Salah ya rasu a Masar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Liverpool ta ƙasar Ingila, Mohamed Salah ya shiga jimami sakamakon rasuwar kakansa, Ahmed Abdel Aziz Al Bambi, wanda ya rasu a yau Litinin, kamar yadda rahotanni daga gidajen jaridun ƙasar suka bayyana. Kawun ɗan wasan, Abdel Aziz Al Bambi wanda kuma shi ne shugaban cibiyar matasa ta Mohamed Salah, ya tabbatar da labarin rasuwar. A wata taƙaitacciyar sanarwa, ya bayyana alhininsa bisa rashin, inda ya kuma nemi al'umma da su sanya shi acikin addu'o'insu wajen nema wa mamacin gafara. Za a gudanar da jana’izar marigayin ne a babban masallacin…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sake ganawa da Fubara da Wike a Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin Shugaba Bola Tinubu ya gana da Ministan Abuja Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas a matsayin wani ɓangare na warware rikicin siyasar da ke tsakanin mutanen biyu. An ruwaito cewa, wasu jagororin siyasa daga jihar sun samu halartar zaman, wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Saidai ba a bayyana abin da zaman nasu ya ƙunsa ba a lokacin haɗa wannan rahoto. Zaman, wanda aka yi ta bayan fage na zuwa ne yayin da wani sabon rikicin siyasa ke shirin kunno kai a Ribas, wanda…
Read More

Remi Tinubu ta yi kira da ƙarin hare-haren Amurka a Nijeriya bayan jinjina wa harin Kirsimeti

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa Nijeriya na buƙatar ƙarin sojoji da haɗin-gwiwar tsaro da Amurka domin yaƙar ƙungiyoyin 'yan ta'adda a arewacin Nijeriya. Remi Tinubu ta kuma bayyana harin Amurka na ranar Kirsimeti a matsayin albarka ga Nijeriya, sannan ta bayyana fatanta na samun ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin ƙasashen biyu. A lokacin da ta kai ziyara Amurka, tsohuwar sanatar daga Legas ta yi tsokaci akan hare-haren sojojin Amurka a Nijeriya guda biyu da aka ƙaddamar da su ta sama a Sakkwato, waɗanda aka nufi wasu wuraren 'yan ta'adda da su. Haka…
Read More

Ramadana: Gwamnan Kaduna ya buƙaci malamai da gidajen jarida su faɗakar akan muhimmancin zaman lafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya buƙaci malaman addinin Islama da kafafen yaɗa labarai da na sadarwar zamani da su yi amfani da watan Ramadan da ke tafe a matsayin wata babbar dama ta ƙarfafa kira da zaman lafiya, haƙuri da haɗin kan ƙasa. Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na kafin Ramadan na 2026 da ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya a babban hedikwatarta da ke Kaduna. Gwamnan wanda Sakataran Gwamnatin jihar, Dakta Mu’azu Meyare ya wakilta, ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziƙi, tsaro da zamantakewa da ƙasar ke…
Read More

An fara zanga-zangar neman wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masu zanga-zanga na taruwa a Abuja domin gudanar da gangamin “Occupy National Assembly” don nuna adawa da ƙin amincewar da Majalisar Dattawa ta yi kwanan nan game da tura sakamakon zaɓe ta na'ura. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun yi cincirindo a wurin, inda aka jibge na hukumomin 'yan sanda, sojoji da na Cibil Defense (NSCDC). Zanga-zangar ta biyo bayan matsayar Majalisar Dattawa ta ƙin amincewa da wajabta tura sakamakon zaɓe ta na'ura. A ranar Laraba, an ruwaito cewa Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da gyaran da aka gabatar ga Sashi na 60,…
Read More

Majalisar Dattawa ta kira taron gaggawa kan yamutsin ƙudirin gyaran dokar zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawan ta sanar da cewa za ta gudanar da zaman gaggawa ranar Talata, 10 ga Fabrairu domin tattauna batun kudirin gyaran dokar zaɓen da ya janyo cece-kuce a faɗin Nijeriya. Rahotanni sun nuna cewa an kira wannan zaman ne sakamakon ƙorafe-ƙorafe da matsin lamba daga jama'ar ƙasa musamman dangane da batun tura sakamakon zaɓe ta hanyar na'ura, wato "electronic transmission of results". Za a gudanar da zaman neda misalin ƙarfe 12 na rana inda aka buƙaci kowane sanata ya halarta. Mutane da dama na ganin matakan ƙin amince wa wajibcin watsa sakamakon zaɓe…
Read More