Haɓakar tattali za ta samar wa rayuwar kowane ɗan Nijeriya sauƙi, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira da gwamnoni 36 na faɗin Nijeriya tare da ministoci da sauran jami’an gwamnati da su yi aiki wajen ciyar da al’umma gaba da haɓakar tattali domin magance matsalolin ‘yan Nijeriya na yau da kullum.

Shettima ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin taron Majalisar Tattali ta Ƙasa (NEC) jim-kaɗan bayan jawabin Shugaba Bola Tinubu, wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A cewarsa, hikimomin da wasu ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi suka yi amfani da su wajen ciyar da ƙasarsu da al’ummominsu gaba, su ya kama Nijeriya ta bi domin inganta rayuwar kowane ɗan ƙasa.

Ya bayyana zaman na kwana biyu a matsayin fage na cigaba da ƙoƙarin aiwatar da yarjejeniyar gwamnati da al’ummar Nijeriya, waɗanda ɓangarori ne na samar da tsarin ci-gaba mai ɗorewa a ƙasar.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu bisa hoɓɓasa da yake yi wajen inganta lamuran tattalin arziƙi ta yadda gyare-gyarensa a fannin suke kawo sauyi mai amfani ga ƙasa da al’ummarta.

Haka kuma, Shettima ya zayyano manufofin da fagen ya tanada domin cimma abin da aka saka a gaba waɗanda suka haɗa da kasuwanci tsakanin shiyyoyi, zuba jari da ababen more rayuwa bisa la’akari da abin da kowace shiyya take da shi.

By Babaji