
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne da aka alaƙanta su da Ƙungiyar Jama’atu Ahlissunnah Lidda’awatu wal-Jihad, sun aike da saƙo mai ƙunshe da barazanar kai hari ga mazauna Ƙauyen Dunshigogo da ke Ƙaramar Hukumar Kaiaman Jihar Kwara.
A cewar rahoton ShaharaReporters, anyi zargin cewa an aika wasiƙar ne kai-tsaye zuwa ga ‘yan ƙauyen, wadda a ciki aka yi gargaɗin cewa mayaƙan za su kai wa mutanen hari.
Wannan ya yi kama da irin barazanar da aka yi ya ‘yan ƙauyen Woro, inda aka halaka mutane 162 a wani mummunan hari da ya auku a makon da ya gabata.
An ruwaito cewa, bayyanar wannan wasiƙa ya jefa firgici acikin al’ummar Dunshigogo, lamarin da ya sa da dama daga cikin ‘yan yankin suke shirin ƙaura sakamakon tsoron kada farmaki ya rutsa da su.
Tuni dai jama’ar gari suka fara rufe wuraren kasuwancinsu da yin cincirindo wajen ficewa dafa yankin.
“Ban san wanda ma zan kira ba yanzu da ba zai yi wa rayukan waɗannan mutanen zagon-ƙasa ba”, inji wata majiya.
A ranar 3 ga Fabrairu ne ‘yan ta’adda suka kutsa ƙauyukan Woro da Nuku da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama inda suka halaka sama da mutane 162, ƙone gidaje da yin awon-gaba da wasu da dama.
