Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Matuƙar za ka kasance ka na jin cewa abin alfaharinka ne Sarki Sunusi ya shiga jami’a don yin degree. Ka na jin cewa an ci amanar Kwankwaso ficewar Gwamna daga NNPP. Ko kuwa kokarin komawar Gwamna APC ba a ci amanar kuri’ar ka a zaben Abba a 2023 ba.
Ko ka rika tunanin Dangote da Abdussamad ba su da hakkin taimakawa Kanawa da scholarships ko start up. Malaman ka komai su ka fada daidai ne, baka duba yadda a aikace sun saba da wa’azukansu.
Tunanin ka kullum addini,addini. Amma ba komai naka a aikace na addinin. Ka na jin babu komai don Yan siyasa sun kasa samar da ruwan sha su na Gina gadoji, ka na tafi kana cewa su na aiki. Da talaka ya yi laifi ka yi wuf ka la’ance shi, Kai ne na farkon nuna juyayi idan iftila’i ya shafi wani babba. Ba ruwanka da bayanan da zasu iya canza rayuwar mutane, Amma kana gaba wajen yada trending issues na influencers.
Ba ka jin takaicin ganin kananan Yara na gararamba a tituna su na bara. Matasa sun tsunduma a shaye-shaye da fadan daba. ’Yan mata na yawon karuwanci ko’ina. Ka gamsu cewa ba ka da wata gudunmuwa da za ka iya bayarwa wajen canja halayya ko tunanin mutanen ka. Matukar matsalar al’umma ba ta dame ka ba, amma kana alfahari da makasanka, kana basu kariya. To, tabbas kai bawa ne. ka zama bawan elites , an bautar da tunaninka!!!
Bautar tunani ta fi bautar jiki illa…domin mai bauta da jiki ya san shi bawa ne wanda zai iya samun fansa wata rana…amma Wanda aka bautar da tunaninsa, a wautar sa kullum gani yake yantacce ne shi, mai yin abinda ya zaba. Zai mutu cikin bauta bai sani ba.
Kaiconka bawan tunani, saboda a cikin bayi kai ne mafi ƙasƙanci !!!
Abubakar manazarci ne a birnin Kano
