Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Cin Amana ya na da manufa biyu, a tsakanin Yan siyasa a siyasance da a tsakanin mutane a mu’amalance. A siyasance halal ne amma tsakanin mutane haramun ne. Don haka idan ta tabbata Abba ya koma APC, bai ci amanar Kwankwaso ba, saboda za mu iya cewa sunnarsu ce ta Yan siyasa. Amma tabbas ya ci amanar talakawan Kano, wadda Allah ba zai bari ba sai ya yi sakayya.
Duk da cewa da gudunmuwar mu aka kafa wannan gwamnati ta NNPP, amma ba a jima da fara aikinta ba mu ka fuskanci akwai lauje cikin nadi. Na shiga kafafen watsa labarai na rediyo, talabijin da jarida, na gargadi Kanawa cewa wannan gwamnatin ta Abba Kabir da alama da cin amanar Kanawa ta shigo mulki, sakamakon aikinta na farko shine rusau, tun kafin ma ta zauna da gindinta.
Ba a taba gwamnati a tarihin Kano wadda babu abinda ta ke haifar mana tun shigowarta banda bala’i da annoba iri-iri kamar ta ba, kama daga annobar tattalin arziki zuwa ta siyasa da zamantakewa. Ku saurari hujjoji na, sannan ina muku addu’ar Allah ya baku ikon kallonsu da idon basira kuma ku yi adalci.
Mun yi gwagwarmaya iya gwargwado wajen ganin an kawar da Gwamnatin Ganduje da mu ke ganin babu talaka a gaban ta, tare da tunanin cewa gwamnatin Kwankwasiyya za ta taimaki Kano. An kai ruwa rana tun a 2019, wanda hakan bai yiwu ba sai a 2023 aka sami nasara da kyar. Amma kafin a je ko’ina sai muka fuskanci cewa wannan gwamnati za ta ci amanar Kanawa. Domin da zuwa, sai ta shigo da fushi, yadda aikinta na farko shine janyowa jihar asarar kimanin biliyan 126 na rusau mara ma’ana mai cike da bi-ta-da-kulli kawai. Domin kusan a duk inda ta yi rusau (Kasuwar kwari, BUK Road, gefen Tituna, cikin GRA dss) gaba dayansu Kwankwaso ne ya fara yanka filayen wurin a baya. Har aka shafe shekarar 2023, jihar Kano daga rantsar da ita zuwa karshen shekara, ba ta iya tara harajin biliyan 126, wato kwatankwacin asarar da ta jaza mana sakamakon rusau. Ku ce min annoba ta daya.
Ana ta zaman makoki a gwamnatance sakamakon shari’ar zabe, amma ana sanar da nasarar Abba a supreme court, sai ya sake jefo mana wata annobar ta masarauta. Wadda ta zo ta raba kan al’umma, ta zubar da kimar sarauta, ta zubar da kimar Kanawa ko ina a duniya, wanda sakamakon hakan ya dabaibaye har ita kanta gwamnatin da Gwamna yadda ya rasa wasu iko a jihar saboda sa-in-sa da tarayya. Wannan annobar har shi kansa ta shafa.
Tun da aka dawo dimokuradiya a 1999, babu wata gwamnati da ta sami kudaden shiga daga gwamnatin tarayya da na harajin cikin gida irinta. Daga 2023 zuwa 2025 ta sami harajin cikin gida biliyan 211. Sannan ta karbi kudade na wata-wata daga tarayya adadin biliyan 141 a 2023, biliyan 190 a 2024 da Kuma biliyan 223 a 2025. Yayinda local governments su ka karbi biliyan 261 a 2023 sannan su ka karbi biliyan 331 daga September 2024 zuwa December 2025, wato a jumlace Gwamnatin Abba ta lakume Tiriliyan 1.3 a shekaru uku (banda kudaden tallafin ecological fund, health intervention dss). Don Allah me za’a nuna wanda a hakika za’a ce lallai an tsinanawa talaka da irin wadannan makudan kudade a shekaru uku idan banda fenti, face-facen tituna, saka solar da gyara gine-ginen gwamnati?
Nawa aka saka a samar da aikin yi ga dimbin matasa da su ka jefa musu kuri’a? Nawa aka saka a harkar noma? Na wa a ka kashe wajen samawa dalibai kujerun zama a makarantun ko magani a asibitoci da samar wa mutane ruwan sha? Amma mun ga irin biliyoyin da a ka ware domin gyara ginin majalisa, ofishin sakataren gwamnati, ma’aikatu, kashe biliyoyi don raba kujerar Haji da sauransu.
Yan kwankwasiyya nawa aka tara aka baiwa jari? amma an ba tsoffin kansiloli ko? Ko a gwamnatin Ganduje bamu ga inda EFCC ta kama jami’an gwamna da tuhumar kudade ba. Scandals nawa aka yi ta kudade a wannan gwamnatin? Akwai annobar da ta kai kana da kudi amma ba za a kashe maka su ta inda ka fi bukata ba? Sai dai ta hanyar bada kwangiloli da zasu azurta kalilan? Kwangilolin titunan ma, sai hanyoyin masu Ido da kwalli a kwaryar birni an bar yankunan karkara a yashe. Kwangila mafi muni shine bada kusan biliyan 7 don gina sabon Dam a Kunci, a jihar da ke da dama-damai 22 wadanda ke barci?
Tattalin arzikin Kano, musamman ta hanyar noma da zuba jari, ita ce hanyar da Kano za ta iya samawa miliyoyin al’umma ayyukan yi da arziki, amma wannan gwamnati babu ruwanta da wannan. Domin tun da Abba ya ci zabe, a kungiyarmu ta NDF mun yi yunkurin zama da shi kafin a rantsar da shi domin ya shigo gwamnati da shirin da zai tallafawa jihar habaka tattalin arzikinta. Domin a yau idan aka tsaida kudade daga Abuja, ko albashin ma’aikata Kano ba za ta iya biya.
Amma ba mu sami damar zaman ba sai dai taya murna kawai. Tun da gwamnatin ta shigo, na zauna da kwamishinoni biyu ido-da-ido na ma’aikatar ruwa tare da baje musu kolin bincike na yadda Kano zata yi amfani da Dama-damai 22 da muke da su don yin noman kifi da zai kawo mata daruruwan miliyoyin daloli. Najeriya na siyen kifin dala biliyan $2.3 duk shekara, Kano na da dam 22 ba’a noman kifi su na barci. Na yi documentary akan dams din mu, na yi feasibility studies akan noman kifi, sannan na samo Yan China wadanda ke son a gayyato su su zuba jari. Amma jami’an wannan gwamnati sun yi biris da maganar.
Bayan an nada sabon sakataren gwamnati, saboda mutumina ne, na je na yi masa presentation na yadda za’a dabbaka noman kifi a Dams din Kano wanda zai iya samawa Kano biliyoyin daloli da ayyukan yi. Shi ma tunda ya ce zai yi magana da Sarkin Shanu, shugaban kwamitin samar da kudaden shiga na jiha, daga nan bai sake daga waya ta ba. A yanzu haka akwai wani wanda ya nemi in magana da mutanen gwamnati domin akwai investors daga Saudi da Turkiya da ke son saka jari a Kano kan harkar solar da bada rancen ayyukan raya kasa na miliyoyin daloli. Abin takaici, wani DG a wannan gwamnatin da kansa ya ke cewa duk wadanda ke kewaye da Gwamna tsoronsa su ke ji.
Domin shi kansa DG din ya na son ganin Gwamna domin ya bashi wani report, amma wadanda aka baiwa aiki domin tsarawa Gwamna abubuwa, duk wanda ya tunkara cikinsu sai ya ce masa ya zo wani taro ya lallaba ya nemi appointment a wurin Gwamna kai tsaye. Ya ilahi idan DG da ke maka aiki ba zai iya ganin ka ba, wane irin mulki kake yi? Kwanan nan fitaccen Jarumin Kannywood Hamisu Iyantama ya saki wani video da ke zargin ya kasa ganin Gwamna duk da irin kusanci su da kuma gudunmuwar da ya baiwa Gwamna a zabe. To, ta yaya kuwa Gwamna zai iya cika alkawuransa idan ya kewaye kansa da Yes-Men da ko schedule dinsa ba za su iya tsarawa ba ballantana policy na jihar.
Babu annoba ga mulki wadda ta wuce kewaye kai da mutanen da sai dai su fada maka abinda kake so kawai. Wannan na cikin annobar da ta hana gwamnatin Abba yin abinda ya kamata da kudaden mu tsawon shekaru kusan uku.
Amma saboda wata irin toshewar basira, sai ka ga wanda ya je makaranta ya waye, na yabon wai ana tituna da saka fitulu a kwaryar birni. Ka je unguwannin Kurna ko Dorayi ko cikin birni ka ga Almajirai da matasa maza da mata wadanda ba su da aikin yi, ba karatu, ba su san me zasu ci anjima ba. A duk watan Duniya muna haihuwar sabbin mutane akalla 27,000. Ba ayi wa na yanzu maganin matsaloli ba ballantana tanadin masu tasowa, don Allah to a haka muke tsammanin wanyewa lafiya a Kano idan aka ci gaba da irin wannan mulki?
A ƙarshe sai ga shi ya zo mana da annobar da ta fi kowacce, wato yin wannan canjin sheka zuwa APC. A wannan lokaci, hakika sauya sheka zuwa APC, zai bashi damar murkushe duk wani ɗan takara a jam’iyyar APC (su Barau da Zaura), sannan zai danne Ganduje a matsayin jagora a jiha, wadanda duk bukatarsa ce. Amma mu Yan jihar Kano wadanda mu ka goyi bayansa ya zama Gwamna, a karkashin zaton zai mana aiki ya ceto mata da matasa, ya san cewa ya ci amanar mu. Irinmu dai saboda tabbatar da Kano a jagoranci kare muradun talaka, wanda shi da maigidansa da Kwankwasiyya ke ikirarin yi, ya sa muka ba shi goyon baya.
Da zaton cewa zai banbanta da yaudara irin wadda Kwankwaso ya zo da ita. Mun yi tsammani Abba zai jajirce wajen kare hakkin talakawa amma sai ga shi ya bi sahun maigidansa ya ma zarce shi wajen cin amanar talaka. Ya nuna karara cewa bukatarsa ce kawai bukata, wanda har gara shi jagora da ke buya bayan talaka ya saka tasa bukatar. Ga iri-irinmu, babu wata cin amana da zata wuce Abba ya koma APC saboda babu irin tofin ala-tsine da ba mu yi mata ba sakamakon matse talaka da azurta kalilan tun daga kan Buhari zuwa yanzu. Kowa ya ga kamun ludayin APC a shekaru 10 cewa ba ruwansu da muradun talaka.
To amma Abba ya kewaye kansa da Yan a bi Yarima a sha kida, ya sa sun tunzura shi ya ci amanar Kanawa, ya butulcewa ni’imar Allah. Domin zaton cewa sai ya shiga APC zai iya zarcewa a mulki, butulcewa ubangijin da ya murkushe masa APC ya bashi mulki ne a karon farko. Amma dai kar mu manta cewa duk wanda zai iya rufe Ido ya ci amanar magoya bayansa ko wadanda su ka zabe shi, to ya zauna da shirin ranar sakamako daga wadanda ya zalunta da kuma ubangiji. Kuma mu sani cewa shi mulki ba jam’iyya ce ke bada shi ba Allah ne, domin ko a zaben da ya gabata a jihar Zamfara munga yadda Matawalle ya ci amanar PDP ya koma APC amma da yake ba jam’iyya ce ke bada mulkin ba ya fadi zaben.
Babban abin takaici a garemu Kanawa a yanzu shine cewa mun yi sakaci yadda Kwankwasiyya da Gandujiyya sun mamaye lamuran siyasar mu. Wannan dambarwar ba karamar dama ba ce ta kassara tasirin Kwankwasiyya da Gandujiyya, amma abin takaici shine bamu da hadin kai da hangen nesan da zamu iya tattaruwa don yiwa Kano wannan Jihadi. Kuma matukar bamu karya wannan tasiri ba, haka dai son ran wadannan bangarori biyu zai yi ta tamaula da mu ya na maida mana jiha baya, su ci gaba da more arzikinmu su na talautar da mu.
Kuma kafin Abba ya ci amanar Kwankwaso, ai shi Kwankwaso ne ya fara cin amanar mu. Domin ba wanda ya cancanci zamarwa Arewa Sardauna irin shi, domin bayan Buhari babu wani Dan siyasa da talaka ke kauna saboda Allah sai Kwankwaso. Amma sai ya maida bukatarsa ba ta al’umma ba kullum ita ce gabansa, shi yasa Allah ya kawo wandanda shi ma za su ci amanarsa (Ganduje da Abba). Kuma duk yadda wani Dan siyasa ya kai da yaudarar mutane ai ba zai kai Buhari ba, kuma mun ga sai da Allah ya yi wa Buhari tsirara kafin ya mutu, kuma har a kabari daga cikin gidansa an ci gaba da yi masa tsirara. Akwai tozartar da ta kai haka? To Kwankwaso ma ya kamo hanyar Buhari.
’Yan siyasa ku wa’aztu ku daina tunanin yaudara mai dorewa ce. Kuma da na gaba ake ganin zurfin ruwa. Mu kuma Kanawa ya rage namu, ko dai mu ci gaba da sakarcinmu na zama bayin siyasar Kwankwasiyya da Gandujiyya ko kuma 2027 mu dawo da martabar da aka san mu da ita tsawon tarihi na siyasar na ki da Malam Aminu Kano ya gina mu akai, wadda Kwankwasiyya ta ci gajiyarta kafin yanzu ta yi watsi da ita. Kano ce kadai ta rage a Arewa maso yamma a tsaye kyam, amma wannan sakarcin na siyasa da mu ke yi ba zai haifar mana da mai Ido ba. Ambaliyar talauci da rashin aiki da barazanar tsaro ta tunkaro mu, ko dai mu nemo shugabanni na gari da zasu saka matsalar mu a gaba ba bukatar su ba, ko ambaliyar da ta cinye makwabtanmu ta hada da mu.
Idan kunne ya ji… jiki ya tsira!!!
Malam Ali manazarci ne a Kano
