09
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ɗalibin ajin ƙarshe (SS3) a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Potiskum da ke Jihar Yobe mai suna Hassan Ahmadu ya rasu a sakamakon lakaɗa masa duka da abokan karatunsa suka yi. Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a jiya Lahadi acikin makarantar, wadda ke Ƙaramar Hukumar Potiskum ta jihar. A cewar wata majiya daga gidan su mamacin mai kimanin shekaru 17, tuni aka yi jana’izarsa a ranar da abin ya faru a garin Gadaka da ke Ƙaramar Hukumar Fika a jihar. An ruwaito cewa, wasu ‘yan ajinsu ne suka farmaki shi…
