Kaduna: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasto bayan halaka jami’an tsaro uku a wani sabon hari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ’yan bindiga a Jihar Kaduna sun yi awon-gaba da wani fasto mai suna Rabaran Fr. Nathaniel Asuwaye da wasu mutum 10 a ƙauyen Karku da ke Ƙaramar Hukumar Kauru.

An sace Faston, wanda shine limamin Cocin Katolika ta Holy Trinity da ke ƙauyen Karku a gidansa da misalin ƙarfe 3:20 na daren ranar Juma’a wayewar Asabar.

A wata sanarwa da Cocin Katolika ta Kafanchan ta fitar, wadda Babban Sakataren cocin, Rabaran Fr. Jacob Shanet ya sanya wa hannu, ta yi tir da harin.

Sanarwar ta ce a lokacin harin, ’yan bindigar sun kuma halaka jami’an tsaro guda uku, waɗanda suka haɗa da Jacob Ɗan’azumi, Maitala Kaura da Alhaji Kusari.

Wasu mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen ne da daddare, inda suka dinga harbe-harbe, kafin su sace Faston da sauran mutanen, sannan suka tafi da su.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba a hukumance akan al’amarin.

Hukumar gudanarwar cocin ta roƙi mabiyanta da sauran jama’a da su yi addu’a domin samun nasarar kuɓutar Faston da sauran waɗanda aka sace cikin lafiya.

Mazauna ƙauyen Karku su yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin sakamakon yawaitar hare-haren ’yan ta’adda.

Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa rahoton domin samum ƙarin bayanai.

By Babaji