Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta bai wa Dikko Raɗɗa digirin girmamawa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Raɗɗa ya yi alƙawarin ba da ayyukan yi nan take ga ɗalibai mafi hazaƙa.

Ya kuma amince da ƙarin albashi ga ma’aikata, da ba da kyautar mota ga ɗalibi mafi hazaƙa a taron yaye ɗalibai na (UMYUK).

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa yabfaɗi haka bayan da jami’an ta karrama shi da digirin girmamawa na Dakta a fannin gudanar da harkokin jama’a (Public Administration) a Katsina.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan karramawa a matsayin kira na ƙara jajircewa wajen hidima, tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa jami’ar jihar, wadda ya bayyana a matsayin cibiyar ilimi, tarbiyya da hidima.

Ya taya ɗaliban da suka kammala karatu murna, tare da bayyana alfahari da rawar da jami’ar ke takawa wajen bunƙasa jarin ɗan Adam a Jihar Katsina.

“Na karɓi wannan karramawa cikin tawali’u da sabuwar fahimtar alhakin da ke kaina na yi wa al’ummar Jihar Katsina hidima da gaskiya da ƙwazo,” in ji shi.

Ya shawarci ɗaliban da aka yaye su kasance masu jagoranci da gaskiya, su ƙirƙira manufa, tare da hidimtawa al’umma ba tare da son kai ba.

“Ku zama jakadu na wannan jami’a da kuma Jihar Katsina. Ku yi amfani da iliminku wajen warware matsaloli, ɗaga martabar al’umma, da kawo sauyi mai kyau a duk inda kuka tsinci kanku,” in ji Dikko Raɗɗa.

Gwamnan ya sanar da cewa mafi ƙwarewar ɗalibai gaba ɗaya za su samu aikin yi kai tsaye bayan kammala hidimar ƙasa (NYSC), inda ya umarci shugaban ma’aikata (Head of Service) da ya gano tare da kammala aiwatar da hakan ga waɗanda abin ya shafa.

“Wannan mataki ne na girmama ƙwarewa da kuma ƙarfafa ɗalibai su nemi mafi girman matsayi a karatunsu,” in ji shi.
Haka kuma, Gwamna Raɗɗa ya amince da bayar da kuɗin kyauta na ₦100,000 ga mafi ƙwarewar ɗalibai a dukkan sassa, yayin da mafi ƙwarewar ɗalibi gaba ɗaya zai samu sabuwar mota ƙirar zamani.

Ya bayyana cewa an saki kuɗaɗe domin tantance shirye-shiryen karatu (accreditation) bisa ƙa’idojin ƙasa da na duniya, sannan ya sanar da ƙarin albashi ga ma’aikatan koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba, a matsayin godiya ga jajircewarsu.
“Gwamnatinmu za ta ci gaba da tallafa wa UMYU domin cimma nagarta, ɗa’a, da hidima ga bil’adama,” in ji shi.

Tun da farko, shugaban jami’ar (Chancellor), Sanata Ibrahim M. Ida (Wazirin Katsina), ya bayyana bikin yaye ɗaliban a matsayin ranar farin ciki, inda ake murnar ƙoƙarin ɗaliban da goyon bayan iyayensu.

Ya yaba wa jami’ar kan ci gaban da ta samu wajen faɗaɗa shirye-shirye, bunƙasa bincike, da ƙarfafa hulɗa da al’umma.

Haka zalika, shugaban majalisar gudanarwa (Pro-Chancellor) kuma shugaban kwamitin gudanarwa, Sanata Hadi Abubakar Sirika, ya gode wa Gwamna Raɗɗa kan jagorancinsa, tare da jaddada ƙudirin majalisar na faɗaɗa damar samun ilimi, ƙarfafa bincike, da sake fasalin jami’ar domin gogayya a matakin duniya.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban jami’a (Vice-Chancellor), Farfesa Shehu Salihu Muhammad, ya bayyana yadda Jami’ar ta bunƙasa daga ɗalibai kusan 1,000 zuwa sama da 20,000, tare da shirye-shiryen digiri na farko da na gaba da digiri guda 117 da ake bayarwa.

Ya yaba wa ci gaban da aka samu na ci gaba da karatu ba tare da tsaiko ba, ingantaccen shugabanci, haɗin gwiwar bincike mai ƙarfi, da cikakken tantancewa (accreditation) ga dukkan shirye-shirye.

Farfesa Muhammad ya taya ɗalibai 2,682 murna, ciki har da masu digirin First Class 31, tare da yaba wa Gwamna Raɗɗa kan biyan albashin ma’aikata cikin gaggawa da ci gaba da tallafa wa jami’ar.

Jakada Ahmed Rufa’i, da ya yi jawabi a madadin duk masu karɓar digirin girmamawa, ya gode wa jami’ar, tare da shawartan ɗaliban da aka yaye su yi wa al’umma hidima da gaskiya da jajircewa.

Taron yaye ɗaliban ya samu halartar mataimakin gwamna, Malam Faruk Lawal; kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Nasir Yahaya Daura; sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari; shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Falalu Bawale; Sanata Muntari Abubakar (Yankin Funtua); shugaban ma’aikatan gwamna, Abdulkadir Mamman Nasir; babban sakataren sirri, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji; Jakada Lawal Kazaure,

Sauran sun haɗa da tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu; babban alƙalin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi; mambobin majalisar Zartarwa ta jihar; shugabannin tsaro; sarakunan gargajiya; da ’yan kasuwa.

Wannan shine karo na 14 da jami’ar ke bikin yaye ɗaliban ta.

By ukarofi