2027: Jihar Ribas ba ta buƙatar gwamna wajen nema wa Tinubu ƙuri’a, inji Wike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya ce al’ummar Jihar Ribas ba sa buƙatar gwamna domin samar wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’a a zaɓen 2027 da ke tafe.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da buɗe hedikwatar jakadun Sabunta Fata ta jihar da sauran ababen walwalarsu kamar ɗakunan taruka da motocin bus domin zirga-zirgar harkokinta.

Ministan ya kuma yaba wa kodinetan shirin na jihar, Desmond Akawor bisa ƙoƙarinsa wajen wayar da kan jama’a akan sake zaɓar shugaban ƙasar, inda ya ce za su aiki tuƙuru wajen ganin an sake zaɓar Tinubu a karo na biyu.

Ya bayyana cewa, aikin shiga lungu da saƙo da mambobin shirin suke yi ya nuna cewa Tinubu ya samu karɓuwa a dukkan ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar don haka “Na faɗa a baya Jihar Ribas ba wajen zuwa ba ne, kuma ina maimaitawa wannan jihar ta Tinubu ce”, inji tsohon gwamnan.

Ministan Abujan ya kuma ƙalubalanci sauran ‘yan siyasa da cewa Ribas ta yi fitintinkau wajen yi wa shugaba Tinubu aiki sakamakon ƙoƙarin da suke yi ba dare ba rana wajen fahimtar da jama’a muhimmanci sake zaɓar shugaban ƙasar a karo na biyu.

“Ba ma buƙatar wani gwamna ya nema wa Shugaban Ƙasa ƙuri’a, ba ma buƙata, muna da sanatoci, ‘yan majalisa, ciyamomi, ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa, ciyamomi APC da PDP, baki ɗaya mun haɗu akan yin hidima”, inji Wike.

By Babaji