
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sama mutane 30 sun rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a safiyar ranar Lahadi a Kwanar Barde da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a Jihar Kano, kamar yadda jami’an yankin suka bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa, hatsarin haɗa da wata tirela da ta nufi Gujungu sakamakon burki da ya ƙwace mata bisa “tuƙin ganganci”.
A yayin haka ne fasinjoji da dama suka raunata waɗanda aka garzaya da su asibitoci daban-daban a sassan jihar inda a yanzu suke karɓar magani.
Da yake tabbatar da al’amarin, Kakakin gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa a wata sanarwa, ya ce hatsarin, wanda aka yi zargin ya faru ne sakamakon tuƙin ganganci, ya yi ajalin sama da mutane 30, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka.
Da yake tsokaci akan al’amarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kaɗuwarsa game da rasa rayukan da aka yi yana mai bayyana hakan a matsayin abin “karya zuci”.
A cewarsa, iftila’in ba ga iya iyalansu ba ne kaɗai, abu ne da ya shafi dukkan al’ummar jihar Kano.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan mamatan da fatan ɗaukar dangana ga iyalana nasu. Sannan, ya yi fatan samun waraka cikin ƙanƙanin lokaci ga waɗanda suka jikkata.
Hallau, gwamnan ya umarci hukumomin gwamnati da su gaggauta shiga cikin al’amarin wajen tabbatar da an bai wa waɗanda suka jikkata kulawar da ta dace da halin da suke ciki ba tare da wani jinkiri ba.
Kazalika, ya umarci mai ba shi shawara akan al’amuran jin-ƙai fa ya tsayu akan al’amarin wajen ganin an bai wa iyalan waɗanda abin ya shafa dukkan tallafin da ya dace.
Har ila yau, Gwamna Abba ya yi amfani da damar wajen gargaɗin masu tuƙa ababen hawa musamman manyan motoci wajen kiyaye ƙa’idojin zirga-zirga a titina.
Tuni tawagogin lafiya da na agajin gaggawa suka bazama zuwa wajen marasa lafiyar da iyalansu yayin da al’umma ke jimamin ɗaya daga cikin munanan haɗurran da aka yi a kwanan nan.
