Sojoji sun ƙwato dabbobi 529 daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A yayin da jami’an tsaro ke ta ƙoƙarin samar da tsaro da zaman lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan, a Jihar Katsina sojojin ayarin Forward Operation Base (FOB) sun samu nasarar ƙwato dabbobi 529 daga hannun ‘yan ta’adda, biyo bayan fafata artabu da su a ƙaramar hukumar Kafur ta Jihar Katsina.

Laftanar Kanal MM Isa, Kwamandan FOB Malumfashi ya jagoranta, biyo bayan samun sahihan bayanan sirri dangane da ’yan ta’adda a yankin kasuwar Sabo ta ƙaramar hukumar Ƙafur.

Ana zargin ’yan ta’addar sun shigo ne daga maƙwabciyar Jihar Zamfara kuma an samu tabbacin cewa Idi-A-Ba-Su-Aiki ne ya jagorantar su, wanda ake zargin ƙanin shahararren jagoran ’yan bindiga Ado Aliero ne.

A wata takardar manema labarai daga Ofishin Kyaftin Abayomi Adisa, nuƙaddashin nataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin Birged ta 17, rundunar sojin Najeriya, ya bayyana cewa, bayan da suka samu wannan bayanin sirri, sojojin FOB Malumfashi ba su ɓata lokaci ba, suka yi gaggawar tattaruwa suka nufi yankin. An ɗauki lokaci ana musayar wuta, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addar tserewa zuwa dazuzzukan da ke kewaye da yankin, tare da ɗaukar wasu daga cikin dabbobin da aka sace.

“Nan take sojojin suka shiga bin sawu cikin himma da ƙaimi, suka cin ma ’yan ta’addar da ke tserewa a tsakanin ƙauyukan Burdugau da Unguwar Mantau a ƙaramar hukumar Malumfashi. Lamarin da ya tilasta musu barin dabbobin da suka sace,” in ji Kyaftin Abayomi.

Bayan gudanar da cikakken bincike a yankin, sojojin sun yi galaba kan ’yan ta’addar gaba ɗaya, suka kuma samu nasarar ƙwato jimillar dabbobi 529, waɗanda suka haɗa da shanu 290, tumaki 238, jaki guda ɗaya da kuma babur guda ɗaya.

Sai dai shanu 14 da ake zargin ’yan ta’addan sun yi amfani da su a matsayin garkuwa sun mutu, sakamakon musayar wuta a yayin artabun. Ba a yi asarar rai ko rauni a ɓangaren sojoji ba, abin da ke nuna ƙwarewa da ingancin aikin sojojin,” a cewar Kyaftin ɗin.

Ya zuwa yanzu dai an miƙa dabbobin da aka ƙwato ga hukumomin da suka dace, domin tantancewa tare da mayar da su ga ainihin masu su. Shugaban ƙaramar hukumar Ƙafur, Surajo Nature da DPO na Ƙafur, Aminu Salihu, su ne masu sa ido kan tantancewa da kuma miƙa dabbobin yadda ya kamata.

Babban kwamandan rundunar soji na shiyya ta 8 kuma kwamandan sashen aiki na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa (Arewa maso Yamma) Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar Paul Koughna, ya yaba da jarumtaka da ƙwarewar da sojojin suka nuna, tare da tabbatar wa al’umma da ci gaba da jajircewar rundunar sojin Najeriya wajen ci gaba da kai farmaki kan dukkan nau’ukan ’yan ta’adda a yankin.

A halin da ake ciki dai, sojojin FOB Malumfashi suna ci gaba da  sintiri a dukkan yankin, domin hana ’yan ta’adda sake yin wata ɓarna.

By ukarofi