13
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta musanta cewa ta yi yunƙurin hana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shiga jihar, inda ta bayyana zargin a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama'a. Idan za a tuna, a wata hira da wata jaridar yanar gizo, na hannun daman Kwankwaso kuma jigo a Jam'iyyar NNPP wato Buba Galadima ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf na Kano da rubut wasiƙa zuwa ga Gwamnatin Tarayya ta neman ta daktar da Kwankwaso daga zuwa Kano. To saidai wannan zargi bai samu zama ba domin kuwa, Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin…
