14
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta amince da buƙatar ƙorafin da aka shigar mata da ke neman ta bayar da izinin yin bincike akan sahihancin takardun karatun Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo. Mai Shari'a Binta Nyako a ranar Juma'a ta amince da hakan a takardar da ɗan gwagwarmaya Emorioloye Owolemi ya gabatar domin neman gano sahihancin takardar kammala sakandarensa ta WAEC. Lauyan ɗan gwagwarmayar, Philemon Yakubi (SAN) ya miƙa takardar bisa hukuncin dokar 'yan samun bayanai sashe na 1, 20 da na 21 a kundin 2011. A yayin hukuncin,…
