Babaji

5698 Posts

Ba za mu karɓi fursunoni kamar wasu ƙasashe ba – Gwamnatin Tarayya ga Amurka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ƙi amince wa ƙulla yarjejeniya da Amurka na karɓar waɗanda aka koro a ƙarƙashin tsarin Shugaba Donald Trump na korar waɗanda ba ƴan Amurka ba zuwa wasu ƙasashe, inda ta ce Nijeriya ba za ta bi sahun Rwanda, Eswatini ko Sudan ta Kudu ba. Da ya ke ganawa da manema labarai, Kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ya tabbatar da cewa matsayar Abuja tana nan yadda ta ke, domin a cewarsa hakan zai haifar da barazana ga harkokin tsaro da tattali. A watan Yuli Ministan ma'aikatar, Yusuf Tuggar ya bayyana cewa…
Read More

Gwamna Abba ya kori mataimakansa biyu bisa hannu a belin dillalin ƙwaya da sauya akalar tallafi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sallamar manyan mataimakansa guda biyu bayan kwamitin bincike ya gano suna da hannu a aikata wasu laifuka. Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya bayyana haka a wata sanarwa, ranar Asabar. A cewar Sakataren, an tsige Abubakar Umar Sharaɗa, wato mai taimaka wa gwamnan kan wayar da kan al'umma akan harkar siyasa bayan gano yana hannu a belin dillalin ƙwayan nan Sulaiman Ɗanwawu, kamar yadda hadimin ya tabbatar wa kansa laifin. A ɗaya gefen, an sallami Tasiu Adamu Al-amin Roba, wato mai taimaka wa…
Read More

Peter Obi na son a mayar da wa’adin mulkin shugaban ƙasa shekara biyar zango ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ya yi kira da a mayar da zangon mulkin shugaban ƙasa shekara biyar da soke tsarin yin zango biyu. Da ya ke magana yayin wata ziyara ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed a ranar Juma'a, Obi ya ce yin hakan zai taimaka wa jagorori wajen mayar da hankali ga harkokin shugabanci madadin shirin sake neman zaɓe. Ya bayyana cewa, a tsarin da ake tafiya a yanzu, shugabanni suna ɓata lokaci mai muhimmanci wajen mayar da hankali akan samun nasara a karo na biyu, wanda yin hakan…
Read More

Kano: Hisbah ta kama wani mutum kan ayyukan bokanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama wani mai suna Taufiq a Unguwar Sabuwar Gandu da ke jihar bisa zarginsa da hannu a ayyukan da suka shafi bokanci. Mataimakin Kwamandan hukumar, Sheikh Mujahid Aminudden ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Juma'a, inda ya ce al'amarin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al'ummar yankin suka yi ta kai wa jami'ansu. Ya ce, bayan mazuana unguwar sun koka ne hukumar ta gaggauta gudanar da bincike, lamarin da ya sa aka kama shi. Ya kuma ce, za a maka shi a kotu bisa zargin sa da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon shugaban PDP kuma ministan Buhari, Audu Ogbeh ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Ministan Noma da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh ya rasu bayan shafe shekaru 78 a duniya. Marigayin ya rasu ne a yau Asabar 9 ga watan Agusta, 2025. A wata sanarwa daga makusantansa, za a sanar da lokacin gudanar da jana'izarsa. Sun bayyana godiyarsu ga abokai, abokan aiki da masu fatan alheri a yayin jimamin rashin. Ogbeh shi ne shugaban jam'iyyar PDP daga shekarar 2001 zuwa 2005, sannan minista ne a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Haka kuma shi ne ministan sadarwa a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Shehu…
Read More

2027: Abinda ya sa Jonathan ya fi cancantar tsayawa takara a PDP – Sule Lamiɗo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya bayyana tshohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Johnathan a matsayin babban zaɓin jam'iyyar PDP a zaɓen 2027 da ke tafe, yana mai kira a gare ta da ta yi ƙoƙarin dawo da shi cikinta. Lamiɗo ya bayyana haka ne yayin hira da gidan telebijin na Channels a ranar Juma'a inda ya ce duk wanda jam'iyyar ta tsayar, ƴan Nijeriya za su ba shi goyon baya. Ya ce, a matsayin Jonathan na wanda ya taɓa jagorantar ƙasar a baya, ya fahimci shugabanci kuma yi aiki da kyau da sauran…
Read More

An sako Sowore daga hannun ƴan sanda

Rundunar ƴan sanda ta saki ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore bayan kiraye-kirayen da aka yi na buƙatar a sake shi. Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasan ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya alaƙanta sakin nasa da nasarar kiraye-kirayen sakin nasa da aka yi. Ya rubuta cewa, "Ƴan sandan Nijeriya sun amsa buƙatar ƴan gwagwarmaya. Yanzu haka an sake ni daga tsare ni da aka yi ba bisa ƙa'ida ba." Saidai, ya ce babu wani abin farin ciki a sakin, "amma ina godiya gare ku da jajircewar da kuka yi ba tare da gajiyawa ba." Da fari, wasu matasa ne…
Read More

Dalilin tsare Sowore a ofishinmu, inji ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan ƴan sanda na tawagar jami'ai na musamman, CO Abayomi Shogunle ya bayyana dalilan da suka sa aka tsare ɗan jarida kuma mai fafutukar ƴancin al'umma, Omoyele Sowore da hukumarsu ta yi. Kwamishinan ya ce, an kama Sowore da tsare shi ne bisa umarni kan zargin sa da ƙin bada bayani a lokacin da jami'an ƴan sanda suke bincike akan wasu al'amura da suka shafe shi. Shogunle ya bayyana haka ne yayin wani jawabi ga masu zanga-zanga da ƴan jarida a Abuja, ranar Juma'a. Da fari Sowore ya amsa gayyatar Sufeton ƴan sanda ɓangaren…
Read More

Asibitin Nizamiye ya ƙaryata batun jinkirin aiki ne sanadin rasuwar Sanata Kontagora

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Gudanarwar Asibitin Nizamiye da ke Abuja ta ƙaryata batun da ke cewa jinkirin yin aiki ga marigayi Sanata Ibrahim Musa Kontagora sakamakon rashin kawo kuɗi akan lokaci ne ya yi sanadin rasuwarsa. Ta ce, babu wani batun yi masa aiki da aka shirya yi a asibitin don haka ba ta da alhaki akan faruwar al'amarin. Sanata Kontagora, wanda ya wakilci Jihar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawa daga 2011 zuwa 2015, ya rasu ne a asibitin bayan shiga dogon suma na tsawon sama da sati guda. Jami'in hulɗa da jama'a na asibitin, Mohammed…
Read More

Aikin layin dogo: Kanawa na godiya ga Shugaba Tinubu

Daga Shehu Mustapha Chaji Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kasance Shugaba dake so da ƙaunar al'ummar Jihar Kano. Ya yi ta nuna haka a aikace tun rantsar dashi a shekarar 2023 ta hanyoyi da dama. 'Yan kwanaki da rantsar da Gwamnatin Kwankwasiyya a Jihar Kano ta kaddamar da Rusau baji ba gani. Shugaba Tinubu ne yabi hanyoyin diplomasiyya ya kawo karshen mafi munin Rusau a tarihin Jihar Kano.Bayan nada Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa, Kanawa da dama sun dace da nada su manyan mukaman Gwamnati, saboda yawan wadanda ya nada…
Read More