Babaji

5698 Posts

Kocin Super Falcons, Madugu da mai tsaron gida Nnadozie sun shiga sahun ƴan takarar Ballon d’Or

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai tsaron ragar tawagar Super Falcons, Chiamaka Nnadozie da Koci Justine Madugu sun shiga sahun ƴan takarar kyautar Ballon d'Or ta 2025. An sanya sunan Chiamaka ne cikin ƴan wasa mata da ka iya lashe kyautar Yachine yayin da aka zaɓi Madugu a jerin waɗanda ka iya lashe na gwarzon mai horaswa na shekarar. Mai tsaron gidan ta Brighton tana ɗaya daga cikin yan wasa biyar da aka zabe su a rukunin. Sun haɗa da Ann-Katrin Berger ta Jamus Germany da ƙungiyar Gotham FC, Cata Coll ta Barcelona, Hannah Hampton Ingila da Chelsea, da…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta gina layin dogo a tsakiyar Birnin Kano da zai lanƙwame Naira tiriliyan 1.5

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin gina sabon layin dogon jirgin kasa na haske a cikin birnin Kano da kudinsa ya kai Naira tiriliyan 1.5. Shugaban Kwamitin Kidaya Kudin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar (Bichi) ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Kano. Ya ce wannan aiki zai rage matsalolin sufuri a cikin birnin Kano, inda ya kara da cewa irin wannan aikin ana ganinsa a kasashen Turai da yankin Asiya, kuma yana da matukar amfani wajen bunkasa tattalin arzikin jihar bayan kammalawa. Hon. Bichi ya musanta rade-radin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu…
Read More

WAEC ta lashe amanta: Kaso 62.96 sun ci jarrabawar 2025

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Cibiyar Gudanar da Jarrabawar Makaratun Yammacin Afirka (WAEC) ta fitar da sakamakon jarrabawa na daidai ga ɗaliban da suka rubuta na 2025 a yau Juma'a. Hakan ya biyo bayan kuren da aka samu a yayin fitar da sakamakon a karon fari. Shugaban WAEC a Nijeriya, Dakta Amos Dangut ya bayyana damawa kan yadda aka samu tsaiko a karon fari wajen fitar da sakamakon, wanda ya nuna an samu gagarumar faɗuwa. Ya ce, hakan ya faru ne musamman kan jarrabawar Turanci ɓangaren canka-canka, wanda ya haifar da sakamakon na kuskure. Bayan gyaran ne aka gano…
Read More

Za a koma ciyar da ɗalibai a makarantu bayan Tinubu ya sake buɗe asusun shirin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta koma cigaba shirye-shiryen da suka shafi kula da walwalar al'umma yayin da shirin ciyarwa ga ɗalibai zai cigaba da aiki da kuma raba kimanin Naira biliyan 493 ga magidanta. Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin sake buɗe asusun Hukumar Kula da Shirin Walwalar Al'umma (NSIPA), wanda aka rufe tun a watan Janairun 2024 bisa zargin badaƙala. Ministan Jin Ƙai, Dakta Yusuf Tanko Sununu ya tabbatar da haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja game da tasirin tallafin ƙasashen akan harkokin da suka shafi jin ƙai a Nijeriya. Aƙalla ɗalibai miliyan…
Read More

Yadda zargin Atiku da mamaye ADC ya jefa ƴan ɓangaren Obi cikin damuwa

ADaga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da Nijeriya ke cigaba da kusantar babban zaɓen 2027, akwai yiwuwar samun ɓaraka acikin jam'iyyar adawa ta ADC da aka ƙarfafa ta haɗakar manyan siyasa. Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ke kan gaba wajen jan ragamar harkokin jam'iyyar. Wasu muryoyi daga cikin jam'iyyar sun zargi Atiku da ƙoƙarin mamaye tsare-tsaren jam'iyyar cikin wani salo da nufin zama wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar. Lamarin da ya sa ƴan ɓangaren Obi suke ganin hakan a matsayin nuna ƙiyayya a gare…
Read More

Rashin tsaro: Mata sun yi dandazo a ƙofar gidan gwamnatin Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗaruruwan mata waɗanda galibinsu tsofaffi da masu shayarwa ne suka kewaye tituna a Gusau, babban birnin jihar Zamfara domin nuna kaɗuwarsu game da munanan hare-haren ƴan bindiga da suka yi ƙamari a ƴan kwanakin nan a sassan jihar. Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun taho ne daga Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda inda suka nufi gidan gwamnatin a Gusau tare da neman a gaggauta dakatar da kashe-kashe da garkuwa da mutane da suka yawaita a yankin. An gudanar da zanga-zangar ne bayan wani irinsa da aka yi a birnin makonni biyu da suka gabata…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga ƙarshe, Mawaƙi Kwam 1 ya bada haƙuri kan lamarin filin jirgin sama

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Daɗaɗɗen mawaƙin nan mai suna Wasiu Ayinde Marshal da aka fi sani da Kwam 1 ya bada haƙuri sakamakon al'amarin da ya faru a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a ranar Talata. A wata sanarwa, Kwam 1 ya bayyana da-na-saninsa game da lamarin, saidai ya musanta batun cewa ya zo ɗauke da giya a wani kofin zuba ruwan zafi, inda a cewarsa ruwa ne ya ke ɗauke da shi a ciki. Ya ce, yana fama rashin lafiyar da ke sanya shi shan ruwa akai-akai, wanda likitoci suak shawarce shi a…
Read More

Yanzu-yanzu: INEC na shirin bai wa fursunoni damar kaɗa kuri’a yayin zaɓuka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da shirinta na bai wa fursunoni damar kaɗa kuri'a a yayin zaɓuka a Nijeriya. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya faɗi haka a yau Juma'a yayin karɓar baƙoncin Kwantirola Janar na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), Sylvester Nwakuche a hedikwatar INEC da ke Abuja. Ya hakaito hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na tabbatar da ƴancin fursunoni na su yi rajista da zaɓe, inda kuma tuni suka nemi NCoS ta fara shirin aiwatar da hakan duba da koken jam'iyyun siyasa game da lamarin. Haka kuma, Farfesan ya…
Read More

Yawancin rukunin gidajen da aka yi watsi da su a Abuja na ma’aikatan gwamnati ne, inji Shugaban EFCC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta ce bincikenta ya nuna cewa da dama daga cikin rukunin gidaje da aka bar su kara zube a Birnin Tarayya Abuja na ma'aikatan gwamnati ne. Da ya ke magana ranar Laraba a Abuja yayin taron tattaunawa akan harkokin tsare-tsare, Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce nan ba da jimawa ba tawaga ta musamman daga gare su za ta fara ziyartar ire-iren kadarorin waɗanda wasun su an jingine su tsawon sama da shekaru goma. Ya gargaɗi lauyoyi da dillalan harkokin cigaban rukunin gidaje da kada…
Read More

Bayan kasa biyan kuɗin aiki miliyan N22.9, tsohon Sanata, Musa Kontagora ya rasu a asibitin Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Sanata a Majalisar Dattawan Nijeriya, Ibrahim Musa Kontagora ya rasu a Abuja bayan fama da rashin lafiya. Marigayin ya rasu a ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025. Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne a Asibitin Nizamiye da ke birnin tarayyar bayan ma'aikatan asibitin sun ƙi yi masa aiki, saboda kasa biyan Dala cikon 15,000, wato Naira miliyan 22.9 akan lokaci. Asibitin ya gabatar wa tsohon sanatan, wanda ya wakilci mazaɓar Neja ta Arewa daga 2011 zuwa 2015 a majalisar kuɗin aiki da adadinsu ya kai kimanin Dala 30,000 inda kaɗai abinda…
Read More