07
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA) ta shigar ƙorafi ga Antoni Janar na Ƙasa (AGF), Lateef Fagbemi da Sufeton ƴan sanda Kayode Egbetokun, inda ta nemi su binciki mawaƙin Fuji, wato Wasiu Ayinde da aka fi sani da K1 De Ultimate bisa tsaurin ido da ya nuna a filin jiragen sama a Abuja, ranar Talata. Kakakin NCAA, Michael Achimugu ya ce yunƙurin Ayinde na tare jirgin ValueJet da ke halin tafiya ya saɓa wa dokar gudanar da harkokin sufurin jiragen sama a Nijeriya. A wata takarda zuwa ga AGF da Sufeton,…
