Babaji

5698 Posts

Abuja: NCAA ta dakatar da direbobin jiragen sama kan saɓa wa dokar kulawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA) ta dakatar matuƙa jirage masu tashin angulu na ValueJet guda biyu bisa saɓa wa dokokin kulawa a filin Nnamdi Azikwe da ke Abuja. A sanarwar da jami'inta na hulɗa da jama'a da kula da kwastomomi, Michael Achimugu ya fitar, hukumar ta ce lamarin ya auku ne sashen tashin jirage, ranar Juma'a, 5 ga Agusta. Bincike ya nuna cewa matukan sun fara tashi ne daga wuraren ba tare da kammala cike ƙa'idodin tashi ba, lamarin da ta kira abinda ka iya jefa rayukan matukan da wasu…
Read More

Tinubu ya taya ɗaliban Nijeriya uku murna bayan nasara a gasar ƙananan ɗalibai ta duniya

Shugaban Bola Tinubu ya taya ƴan matan nan uku da suka nuna bajinta a wata gasar 'TeenEagle' da aka yi a Birtaniya. Ɗaliban sune Nafisa Abdullahi mai shekara 17 wadda ta haskaka a gasar Turanci yayin da Rukayya Muhammad Fema mai shekara 15 ta fi kowa hazaƙa a muhawara da Hadiza Kashim Kalli da ta lashe kyautar mafi fikira. Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yaba wa matasan saboda bajintar da suka nuna a gasar . Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa makarantu da sauran cibiyoyin karatu, inda ya ce irin waɗannan nasarori…
Read More

NNPC ya sake rage farashin fetur kwanaki biyu da hauhawarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya rage farashin lita a gidajen mansa kwana biyu da tashinsa a kasuwa. Blueprint ta ruwaito cewa, an koma sayerwa akan N900 daga N955 a gidajen man, kamar yadda aka gani a yankunan Gwarimpa, Kubwa, Wuse Zone 6 da Wuse Zone 4 da ke birnin tarayya Abuja. Hakan ya nuna an samu ragin N55 ga kowace lita bayan da farashin ya koma N955 a ranar Litinin. Haka ma a wasu gidajen mai na ƴan kasuwa irin su Ranoil da Empire Energy da ake sayerwa a N950 da N955…
Read More

NiMET ta yi hasashen ambaliya a jihohi 19

Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen za a shafe kwana biyar ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ka iya janyo afkuwar ambaliya a sassan jihohi guda 19 da kuma wasu wurare 76 a faɗin Nijeriya. Gargaɗin da aka fitar daga Ma'aikatar Kula da Muhalli, ya buƙaci masu ruwa da tsaki da mazauna yankunan da lamarin ka iya shafa da su ɗauki matakan kariya. Hakan na zuwa ne yayin da mummunar ambaliya ta afku a jihohin Ogun da Gombe yayin da wasu jihohin da suka haɗa da Legas da Filato da Anambra da Delta da…
Read More

Matar MKO, Doyin Abiola ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar tsohuwar ƴar jarida kuma matar marigayi MKO Abiola, Dakta Doyin Abiola ta rasu bayan shafe shekaru 82 a duniya. Wasu daga cikin iyalanta sun tabbatar da cewa marigayar, wadda tsohuwar Darakta Manaja ce a babbar jaridar ƙasa 'National Concord', ta rasu ne da misalin ƙarfe 9:15 na dare a ranar Talata bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci. Dakta Doyin ta kafa tarihi na zama edita mace ta farko a tarihin aikin jarida a Nijeriya wadda ta bada gagarumar gudunmuwa a fannin. Ta yi karatun digirinta na farko a tsangayar Turanci…
Read More

Pantami ya kirayi Tinubu ya karrama yarinyar da ta yi ta ɗaya a gasar Turanci kamar ƴan wasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya karrama Nafisa Abdullah Aminu, wadda ta zama gwarzuwa a gasar Turanci ta duniya da aka yi a Landon, irin yadda ya yi wa ƴan wasan Super Falcons da D'Tigress a lokacin da suka yi nasara. Nafisa, mai shekaru 17 ɗaliba ce a makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC) da ke Jihar Yobe, inda ta yi nasarar doke sama da ɗalibai guda 20,000 daga ƙasashe 69 ciki har da masu amfani da Turanci. Lamarin da ya sa ake jinjina mata duba…
Read More

Yanzu-yanzu: Bello Turji ya miƙa wasu makamansa da sako mutane 32 a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji ya miƙa wasu daga cikin makamansa tare da sako wasu mutane guda 32 da aka yi garkuwa da su a matsayin wani ɓangare na shirin sulhu da malamai a Jihar Zamfara suka samar. Malam Musa Yusuf, wanda ya shahara da Asadus-Sunnah, ya bayyana hakan yayin wani majalisin karatu a Kaduna, ranar Litinin. Malamin ya ce, Bello Turji ya kuma miƙa wasu daga cikin makamansa bayan wata ganawa a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. Asadus-Sunnah ya bayyana cewa, al'ummar Shinkafi da tawagarsa ta…
Read More

Legas: ‘Yan sanda sun gurfanar da sanannen makashi, Olori Eso kan manyan laifuka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an ƴan sanda a Jihar Legas, sun yi nasarar cafke Wasiu Akinwande, wanda shahararren makashi ne da ya addabi wasu yankuna, inda suka gurfana da shi a wata kotun shari'a da ke yankin Ogba a jihar, bisa tuhumar sa laifuka 11 masu alaƙa da kisan kai, mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba da cin amanar ƙasa da sauransu. Kakakin rundunar ƴan sandan, Benjamin Hundeyin ya bayyana haka a wata, ranar Talata. Ya ce, Akinwande, wanda ya shahara da suna Olori Eso, shi ne ɗan ta'addan da aka fi nema ruwa-a-jallo, inda aka kama shi…
Read More

Ebonyi: Gwamna Nwifuru ya dawo da jami’an gwamnati 81 bayan dakatar da su

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya cire dakatarwar da ya yi wasu manyan jami'an gwamnati su guda 81 a jihar. A sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa, Monday Uzor ya fitar, gwamnan ya umarci kwamishinoni da manyan mataimaka da manyan sakatarori da aka dakatar da su a ranar 28 ga watan Yuli, 2025 da su koma bakin aikinsu nan da nan. Daga cikin waɗanda dakatarwar ta shafa akwai Antoni Janar, kwamishinoni 25, manyan sakatarori 22, manyan mataimaka 14 da kuma mataimaka 24. Rahotanni sun bayyana cewa hakan bai rasa nasaba da rashin halartar wani zama…
Read More

‘Yar shekara 17 daga Yobe ta zo ta ɗaya a gasar Turanci ta duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ƴaƴan ƙasa ke cigaba da ƙara wa Nijeriya kwarjini a idon duniya a ƴan kwanakin nan, ƴar shekara 17 mai suna Nafisa Abdullah Aminu daga Jihar Yobe, ta zama gwarzuwa a gasar 'TeenEagle Global Finals' a ɓangaren salon sarrafa harshen Turanci, wanda aka gudanar a Birnin Landon. Rahotanni sun bayyana cewa, Nafisa, wadda ta wakilci Nijeriya daga makarantar 'Nigerian Tulip International College' (NTIC), ta doke sama da ɗalibai guda 20,000 daga ƙasashe 69 ciki har da waɗanda Turancin ne babban yarensu, lamarin ke ƙara fito da darajar ƴan Nijeriya a gida da…
Read More