05
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da gwamnatin Amurka ke ƙoƙarin tabbatar da kiyaye dokokin mallakar biza ga ɗalibai, ofishin kula da harkokin Amurka a Nijeriya ya gargaɗi ɗaliban Nijeriya da ke karatu a Amurka da su guji saɓa wa dokokin, inda yin hakan ka iya sa a ƙwace wa mutum biza da hana shi shiga ƙasar nan gaba. A ranar Litinin ofishin ya bada gargaɗin ta shafinsa na X sakamakon matsi game da harkokin shige da fice a Birnin Washington akan ɗaliban ƙasashen waje musamman ƴan Nijeriya da sune suka fi yawa. "Idan ka bar makaranta, ka ƙi…
