03
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana zargin Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Bayo Ojulari ya yi murabus a matsayin abinda ta kira da 'ƙarya kuma shirme'. Da ya ke ganawa da jaridar DAILY POST, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Sunday Dare a ranar Asabar, ya ce babu gaskiya akan cewa an tilasta wa Ojulari rubuta takardar murabus. Ya yi ikirarin lamarin wanda ya auku a daren ranar Juma'a wayewar Asabar ya ƙunshi Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC Ola Olukoyede da Darakta-Janar na DSS Adeola Ajayi. Muryoyi…
