01
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Ilimi, Ali Pate, ya ce Ƙungiyar Ungozomomi ta Ƙasa (NANNM) ta janye yajin aikin gargaɗi da ta shiga kwanaki biyu da suka gabata a faɗin Nijeriya. Pate ya bayyana haka ne ga manena labarai jim-kaɗan bayan kammala wani zaman sirri da ya ƙunshi jagororin ƙungiyar a Abuja inda aka cimma yarjejeniya akan wasu al'amura da suka shafi batun. A ranar 29 ga watan Yuli NANNM ta tsunduma yajin aikin bayan abinda ta kira da gazawar gwamnati na amsa gargaɗin da ta bayar wanda ya ƙare a ranar 14 ga watan. Ƙungiyar ta fara…
