31
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata wasu ƴan bindiga suka farmaki jami'an haɗaka na sojoji da ƴan bijilante a yankin Dogon Ruwa dake Gundumar Bashar na Ƙaramar Hukumar Wase a Jihar Filato. Lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan sojoji biyu da ƴan bijilante biyu. Shaidu sun ce, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na dare a lokacin da jami'an suke sintiri a yankin sakamakon samun rahoton yunƙurin kai hari daga ƴan ta'adda. Maharan sun halaka jami'an ne a lokacin da suka yi shigar ba-zata da yi musu ruwan alburusai. Sarkin Dogon Ruwa, Abdullahi Yakubi…
