29
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Jihar Kogi ta samo gawar Ayo Aiyepeku, wanda ɗan jarida ne a ɓangaren ɗaukar hoto bayan halaka shi da wani abokin aikinsa mai suna Oulwapelumi ya yi. Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa Kakakin ƴan sandan jihar Kogi, Williams Ovye-Aya ya tabbatar da faruwar al'amarin a Lokoja, Babban Birnin jihar, ranar Litinin. Ya ce, an gano gawar mamacin ne a yammacin ranar Lahadi a wani yanki da ke kusa da ofishin WAEC da ke Crusher Zone 8 a Lokoja. Daga nan ne aka garzaya da ita zuwa Babban Asibitin 'Specialist'…
